‘Yan Sandan Kasar Hadaddiyyar Daular Larabawa sun kama wani dan Jihar Kano da Katin ATM 30 a Kasar.
1 min read
Rahoton da wata jarida mai suna almazilin ta fitar, ta bayyana cewa, tin da fari matashin mai suna Salisu Ibrahim Rijiyar gwangwan,wata hatsaniya ce, ta hadashi da wani dan kasuwa a kasar,lamarin da ya haddasa ‘yansa kai samame gidan da matashin yake kwana.
Rundanar ‘yan sandan kasar ta ce ta kama matashin da katin ATM guda 30,Wanda dauke yake da sunaye da ban da bam.
A cewar rundanar matashin ya aikata Babban laifin mallakar ATM 30 Wanda wanda yake dauke da suna iri-iri.
A cewar rundunar zata ake da sako, zuwa ofishin jakadancin Nigeria a kasar domin nemo mutanan da suka bawa matashin katikan cirar kudi na ATM, Wanda hakan ya sabawa doka.
Rundanar ta kara da cewa karo na 70 kenan tana kama ‘yan Nigeria a kasar da laifin mallakar ATM din da ba mallakinsu ba.
A cewar Salisu rundanar ‘yan sandan bata bashi damar kare kansa ba,a bisa zarge-zargen da ake masa na fada da wani dan kasuwa da kuma mallakar katikan ATM din ba.