Ƴan fashin daji sun kashe mutum 1,126 a wata shida a arewacin Najeriya
3 min read
Kungiyar kare haƙƙin bil’adama ta Amnesty Intanertional ta ce ƴan
bindiga masu fashin daji sun kashe kimanin mutum 1,126 a jihohin
arewacin Najeriya tsakanin watan Janairu zuwa Yuni.
A rahoton da ƙungiyar ta fitar ranar Litinin, ta ce ɗaruruwan mutane
ne aka raba da gidajensu a jihohin Kaduna da Neja da Katsina da
Filato da Taraba da kuma Zamfara inda aka ƙone gidaje aka kuma
sace mutane.
Amnesty ta ce tun 2016 take bibiyar matsalar ƴan bindiga masu
fashin daji da kuma rikicin makiyaya da manoma.
Ƙungiyar ta ce hukumomin Najeriya sun bar mutanen karkara a
hannun ƴan bindiga da suka kashe ɗaruruwan mutane, wanda kuma
ke ƙara haifar da tsoro da fargaba kan wadatuwar abinci a yankunan
karkara.
Hukumomin Najeriya da suka musanta rahoton Amnesty, zuwa
yanzu ba su fitar da wani martani ba game da rahoton ƙungiyar. Amnesty ta ce ta tattara bayanan rahotonta ne bayan tattaunawa da
mutane a Kaduna da Katsina da Neja da Filato da Sokoto da Taraba
da kuma Zamfara, waɗanda suka shaida mata cewa an bar su suna
rayuwa cikin fargaba da tsoron hare-hare da garkuwa da su yayin da
matsalar tsaro ta ƙara ƙamari a yankunan karkara.
“Yawancin waɗanda aka yi hira da su sun ce sai bayan awanni da
harin da ƴan bindiga suka kawo sannan jami’an tsaro ke zuwa duk
da ana sanar da su cewa an kawo hari,” inji rahoton na Amnesty.
Ta ce kuma “Wani hari da aka kai a Unguwan Magaji a jihar Kaduna,
jami’an tsaro da suka zo suka ga irin makaman da ƴan bindigar suke
ɗauke da su sai suka tsere. Daga baya da suka dawo, akalla mutum
17 aka kashe.”
Amnesty ta ce ta tattara bayanai kan yawan hare-hare da satar
mutane da aka yi a jihohi da dama na arewa maso yamma da tsakiyar
Najeriya a 2020.
‘An sace mutum 380 a Kaduna da Neja da
Nasarawa da Katsina da Zamfara’
Ta kuma ce kudancin Kaduna ne mafi muni inda ƴan bindiga suka
kashe aƙalla mutum 366 a wasu jerin hare-hare tsakanin Janairu
zuwa Yulin 2020.
Ƙungiyar ta bayyana damuwa kan yadda ba a hukunta masu yin
wannan kashe-kashe. “Yadda babu wani da aka hukunta kamar
rashin adalci ne ga mutanen karkara waɗanda suke jin an fallasa su,
in ji Osai Ojigho shugaban kungiyar Amnesty a Najeriya.
Amnesty ta kuma ce duk da matakan da gwamnatocin arewa ke
ɗauka kamar kafa dokar hana fitar dare amma hakan bai dakatar da
hare-haren da ƴan bindiga ke kawai ba kusan a kullum, inda ta ce
hare-haren sun tilasta wa manoma tsere wa daga gidajensu da
gonakinsu a wasu yankuna na Katsina.
“A Katsina akalla mutum 33,130 aka raba da gidajensu waɗanda
suka warwatsu a sansanoni wasu kuma sun koma wajen ƴan
uwansu a birane. Daruruwan manoma sun kasa yin noma a daminar
2020,” a cewar rahoton Amnesty.
Haka kuma rahoton ya ce akalla mutum 380 aka sace domin neman
kudin fansa a Kaduna da Neja da Nasarawa da Katsina da Zamfara,
yawancinsu mata da yara.
Amnesty ta yi kira ga hukumomin Najeriya su ƙaddamar da bincike
kan waɗannan kashe-kashe tare da tabbatar da an gurfanar da
waɗanda suka aikata.
“Yawan kashe-kashe alama ce ta gazawar hukumomi kan haƙƙinsu
na kare rayukan mutane. Ƙaruwar kashe-kashe a arewacin Najeriya
ya nuna gazawar gwamnati.