September 22, 2023

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

An gano dalilin da ya sa iyaye ke gargame ‘ya’yansu

4 min read

Watan Agusta na 2020 na cike da wani sabon juyin na kubutar da
mutane a arewacin Najeriya, kwatankwacin wanda aka fuskanta a
karshen shekarar da ta gabata inda aka ringa kubutar da daruruwan
mutane daga gidajen mari.
A wannan karon, ‘yan sanda da kungiyoyin kare hakkin bil adama ne
suka dukufa wajen kubutar da mutanen da iyalensu suka kulle su, a
cikin mummunan yanayi.
Lamarin ya fara ne a watan Satumbar 2019 yayin da ‘yan sanda suka
gano wani gidan gyaran tarbiyya ko kuma gidan mari a garin Kaduna
ba tare da sahalewar hukuma ba, inda aka sanyawa wasunsu mari.
Kusan mutum 500 ne aka kubutar a jihohi biyar. To amma a 2020 lamarin ya sauya daga wuraren da ake tsare
mutane da dama, zuwa gano inda iyalai suke 12 ga Agusta: ‘Yan sanda sun kubutar da wani yaro Jubril Aliyu
mai shekara 10 wanda ake zargin mahaifinsa da daure shi a
turken dabbobi
14 ga Agusta: ‘Yan sanda sun ceto Ahmad Aminu mai shekara
30 bayan tsare shi tsawon shekara uku
20 ga Agusta: ‘Yan sanda a Kano suka kubutar da wani wani
mutum mai shekara 55, wanda danginsa suka tsare shi tsawon
shekara 30 saboda matsalar kwakwalwa
20 ga Agusta: Salisu Muhammad mai shekara 45 da ‘yan sanda
suka kubutar a Sokoto. Rahotannin sun ce dan uwan mahaifinsa
ne ake zargi ya tsare shi har tsawon shrkara 25. Danginsa sun ce
yana fama da matsalar kwakwalwa.
Halin da aka samu mafi yawan mutuanen dai yana da tayar da
hankali. Da damansu a dakin suke ba fita ko ina tsawon shekaru, a
nan suke kashi da fitsari, a nan suke rayuwa cikin kazanta da yanayi
mai ta da hankali.
Tuni dai ‘yan sanda suka tsare iyaye ko dangi na kusa na mutane da
aka kulle a gida, domin amsa tambayoyin da kuma gurfanarwa gaban
kotu, yayin da su kuma mutanen da aka tserar ke samun kulawar
likitoci.
Jama’a da dama dai na ganin cewa baya ga wadannan, za a iya
samun mutane da dama da danginsu suka tsare su a gida, wasu a
cikin mawuyacin hali, tare da hana musu duk wani ‘yanci na walwala. Me ya sa iyaye ke kulle ‘ya’yansu?
Faruwar lamuran dai suna taso da tambayoyi da dama kan dalilan da
za su sa iyaye su kulle ‘ya’yan cikinsu a cikin irin wannan mawuyacin
hali.
Iyaye ko dangi na fakewa da matsalar kwakwalwa ko kuma shaye-
shaye a matsayin dalilan da suke sa iyaye na tsare ‘ya’yan nasu, to
sai dai wasu na ganin sam wannan ba dalili ba ne na ci musu zarafi.
Wani masanin zamantakewa a Jami’ar Usman Danfodiyo Sokoto
Dokta Usman Abdulkadir ya ce, mafi yawan mutanen ake tsarewa
suna zaune ne ba tare da iyayensu mata ba.
“Suna zama ne da matan mahaifansu, saboda rabuwar aure ko kuma
mutuwa.”
Ya ce “a mafi yawan lokaci, ko da uban yana gida, mata ne ke kula da
abubuwan da suke faruwa a gidan, kuma da wuya iyaye maza su iya
magana.”
Masanin bai amince da masu cewa ana tsare mutanen don gyaran
tarbiyya ba, ko kuma saboda a yi musu maganin matsalar
kwakwalwa ba.
“Gidajen ba asibitoci ba ne, idan mutane suna fama da matsalar tabin
hankali, akwai asibitoci da ya kamata a kai su domin samun kulawa.
”Dubi yaron da aka ceto a Kebbi, halayyarsa ta sauya ta sha banban
da ta mutane. Cin zarafin bil adama ne,” a cewar Dr. Usman.
Ya kara da cewa, mutane da dama suna yin aure ba tare da za su iya
daukar nauyin da ya rataya a wuyansu ba, don haka ne suke gaza ba
su kulawar da ta kamata wajen ciyarwa da samar da matsugunni.
Shin gwamnati ta gaza ne?
Dokta Usman Abdulkadir ya ce gwamnati na da hannu a cikin
wadannan matsaloli, saboda yadda ta mamaye komai, yayin da
dukiya kadan take tafiya ga jama’ar da ake mulka.
Ya ce cin hanci da rashawa sun sa gwamnati ta gaza sauke nayin da
ke kanta a fannin tattalin arziki da lafiya da ilimi da kuma noma.
Sannan hukumomi a duka matakai ba sa mai da hankali wajen samar
da cibiyoyin kula da masu laluran kwakwalwa da ta gyaran tarbiyya
kamar yadda ake bukata.
Mafita
“Wajibi ne gwamnati ta tabbatar da cewa an samar da isassun
cibiyoyin gyaran tarbiyya a duka matakai, a cewar Dokta Usman.
Masanin ya kara da cewa wajibi ne mutane su yi kyakkyawan tsari
gabanin aure kan yadda za su kula da iyalensu. Hakan a cewarsa zai
ba su damar bibiyar duk wani hali da iyalensu suke ciki, da kuma ba
su kulawar da suke bukata.
Ya kuma ba da shawarar cewa wata hanyar kawo karshen matsalar
ita ce idan makota sun lura da an kulle wani, to su kai rahoto ga
hukumomi domin daukar matakan da suka kamata.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *