An kama dagaci da kwamandan Hisbah bisa zargin sayar da jariri
2 min read
Hukumar da ke yaƙi da fatauci tare da bautar da al’umma ta NAPTIP a Najeriya, ta ce ta kama shugaban Hisbah na ƙaramar hukumar Fagge a jihar Kano da ke arewacin ƙasar bisa zargin siyarwa da wata mata wani yaro. Shugaban hukumar ta NAPTIP shiyyar Kano, Shehu Umar ya shaida wa BBC cewar sun gayyaci shugaban Hisbah na ƙaramar hukumar Fagge, da mai unguwar sabon Gari, bisa zargin siyarwa da wata mata Mrs Loveth Jamilu yaron da ta tafi da shi jihar Imo bayan basu naira dubu 20. A cewar Shehu Umar lamarin ya ci karo da sashe na 21 na hukumar NAPTIP da ke cewar duk wanda aka samu da laifin sayarwa ko satar mutum zai fuskanci hukuncin ɗauri a gidan yari na tsawon shekara huɗu tare da biyan tarar naira miliyan biyu. “Muna nan dai (makon) da ya wuce, Hisbah suka kawo wata mata,
Loveth kuma ta je garinsu ba ta dawo da yaro ba, da muka fara
bincike sai muka gano cewa ta samu yaron ta hannun kwamanda na
Hisbah na Fagge da mai unguwa.
“Sai muka gayyace su suka zo nan, da suka zo sai bincike ya nuna
cewa akwai takarda da aka ba wa matar, akwai sa hannun
kwamanda da na mai unguwar waɗanda suka ba ta yaron nan amma
ta ba su kuɗi,
“Ta ba kwamandan Hisbah da mai unguwa N20,000 amma mun
tambayi kwamandan Hisbah ya ce bai karɓi komai a hannunta ba.” in
ji Shehu Umar.
Sai dai hukumar ta Hisbah ta ƙaryata rahoton cewa shugaban
hukumar na Fagge ne ya sayar da yaron.
Babban kwamandan hukumar Harun Ibn Sina ya ce “bibiyarmu da
bincikenmu ya tabbatar da cewa ba haka abin yake ba, ba sayar da
shi aka yi ba, yaron sai da ya zauna a ƙarƙashin hukumar Hisbah
wajen wata takwas ana kulawa da shi ba a samu kowa nasa ba, ana
ta kulawa da shi”.
“A karshe aka samu wanda suka ce suna so za su karɓi wannan yaro
su ci gaba da kulawa da shi.
“Mai unguwar Sabon Gari shi ya yarda cewa za a miƙa wannan yaron
hannun Jamila Kabir, wata mata haifaffiyar nan (Kano) aka yi
yarjejeniya tsakanin kwamandanmu da mai unguwa da ita Jamila
Kabir amma duk wata ɗaya za a dawo da shi mu riƙa ganin halin da
yake ciki wanda da ma ita ce doka.” in ji Ibn Sina.