June 23, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Bamu bawa ‘Yan sanda ko ‘yan Hisba damar Kama Malaman Islamiyya ba -Kano Tsangaya

1 min read

Shugaban hukumar kula da makarantun islamiyya ta jihar Kano,ya musanta zargin da ake ya dawa cewar, gwamnatin jihar kano ta saka hukumar Hisba da ‘yan sandan jihar kano fara kama malaman islamiyyar da suka bude Makarantun islamiyya a nan kano.

A cewar sa labarin kanzan kuregene, duk da cewa gwamnatin bata bada umarnin malaman su bude makarantun ba,amma babu wani umarni data bayar na cewa wasu daga cikin jami’an tsaro su kama malaman ba.

A cewar sa labarin da ake ta fitowa musamman a shafukan sada zumunta na facebook da sauransu babu hannun gwamnati ciki lamarin kuma labarin bashi da makama ballanta tushe.

Ya kuma bakuci malaman dasu ci gaba da bada hadin kai domin tabbatar da cewa jihar Kano tayi sallama da annobar Covid 19.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *