June 23, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Daliban Najeriya sama da 100 aka hallaka

1 min read

Zargin hallaka dalibai ‘yan Najeriya da ake tura wa karatu Cyprus ta
Arewa ya kasance abin da ‘yan ƙasar ke tafka muhawara a kai da ba da
bahasi a shafukan sada zumunta.
Wannan na zuwa ne bayan Shugabar hukumar ‘yan Najeriya mazauna
ƙasashen waje Abike Dabiri-Erewa ta gargadi iyaye kan tura ‘ya’yansu
ƙasar don karatu.
Miss Abike ta yi wannan gargadin ne bayan Hon. Justice Amina Ahmed
Bello, mahaifiyar wani dalibi da ya mutu a yankin ta kai mata koke.
Mutuwar dalibi Ibrahim Khaleel da ke karantun Injiniya, wanda kuma
ake zargin kashe shi aka yi a kasar ya sake bayyana irin hadarin da ake
gani ‘yan Najeriya ke ciki a wannan kasa.
Abike ta jadada cewa mutuwar Khaleel, wanda ke zango na uku na
karantun Injiya, ta sake fito da hali da bankado da yada ake kashe ‘yan
Najeriya babu ƙaƙƙautawa a Cyprus ta Arewa ba tare da sanin dalili ba.
Hukumar da Abike ke shugabanta ta ce sama da ‘yan Najeriya 100 aka
kashe Cyprus ta Arewa, wanda abin damuwa ne sosai, sai dai kokarin
tura wakilai ko tattaunawar diflomasiya domin bincike abu ne mai
wahala saboda yankin ana masa kallon wani bangare ne na kasar
Turkiyya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *