July 12, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Nayi da nasani abisa tsinewa kaina da nake a fina-finan hausa-mai Sana’a

2 min read

Fitaccen jarumin barkwanci a fina-finan Hausa na Kannywood, Musa
Mai Sana’a, ya ce yana matukar nadama a game da tsinewa ko
la’antar kansa da ya ke a cikin wasu fina-finansa da ya yi.
A cikin wata tattaunawa da BBC ta Instagram, Mai Sana’a ya ce a da
ya yi hakan saboda rashin kwarewa.
Amma a hankali- a hankali sai ya fahimci cewa wannan abu da ya ke
fa ba abune mai kyau ba.
Ya ce “Da farko-farkon fina-finai na na yi ta yin abubuwa wadanda ni
a ganina dai-dai ne, amma daga bisani bayan da wasu mutane suka
ja hankalina a kan abubuwan musamman zagi ko tsinewa kaina da
nake, sai na fahimci cewa lallai yakamata na daina”. Musa Mai Sana’a, ya ce a yanzu ya kara fahimtar abubuwa a fina-
finan hausa na Kannywood, kuma ga girma ma da yazo.
Don haka dole wasu abubuwa a jingine su a daina, musamman da
ya ke ga shi an fara tara iyali dole a daina wasu abubuwan a cikin
fina-finai inji jarumin. Mai Sana’a ya ce, shi a fina-finansa ana gani kamar yana wuce gona
da iri, to sam shi ya ba ya haka.
Ya ce, “Ina yin fina-finai na ne domin nishadi da kuma fadakarwa,
kuma na fi yin fina-finai ne ma a kan batun da ya shafi iyaye da
‘ya’yansu”.
Duk abin da aka nayi a cikn fim to fadakarwa nake domin masu irin
wannan hali da na yi a ciki fim su dauki darasi su daina inji Mai
Sana’a.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *