June 23, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Rundunar ‘Yan sandan Kano, na neman wata Mata wacce ke kona wata karamar yarinya da a shana-Kumbotso

1 min read

Yarinyar mai shekaru tara,ta kasance marainiyya domin kuwa iyayenta sun rasu wato bata da Uwa bata da uba,tana hannun ‘yar uwar mahaifinta ta wajen uba.

Haka zalika wannan mata na kunna ashana a jikin yarinyar,wanda hakanne ya sanya jikin yarinyar duk ya kone.

Yarinyar ta kuma ce duk sanda tayi futsari, sai matar ta konata da ashana wanda hakanne ya haifar da konewar jikin yarinyar.

Wata ma’aikaciyyar lafiya dake asbitin Murtala ita ce,ita ce ta fallasa wannan lamari.

To sai dai kwamishiniyyar ma’aikatar al’amuran mata ta jihar kano,Dr Zahra’u Muhammad Umar ta ce, sun dauki nauyin gudanar da rayuwar yariyar,inda ta bukaci mata dasu sani cewa hakkin maraya Allah baya barinsa.

A jihar Kano dai an sha samun irin wadannan matsaloli a kano.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *