June 13, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Wani mai babbar mota ya bi takan wasu motoci a titin Kabuga.

1 min read

Wani hadarin mota da ya faru a Kofar Kabuga zuwa hanyar jami’ar Yusuf Maitama Sule a nan Kano ya yi sanadiyyar raunata mutum guda tare da lalata moroci uku da yi karo da juna.
Shaidun gani da ido sun ce wata karamar mota kirar toyota Corolla ce ta yi taho mu gama da wata babbar mota kirar DAF, inda Toyota din ta kifa, sannan DAF din ta doki wata babbar motar daukar yashi da ke tafiya a daya hannun.
INSERT
Direban karamar motar ya yi karin haske kan abinda ya faru bayan da aka zakulo shi daga karkashin motar.

KO da yake jaridar bustandaily ta yi yunkurin jin ta bakin direban DAF din bai amince da nadar muryarsa ba, sai dai wani daga cikin wadanda suke cikin motar ya tsokaci kamar haka

Hukumar kare afkuwar hadura ta kasa reshen jihar kano ta tabbatar da faruwar lamarin.inda ta ce tana ci gaba da gudanar da bincike.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *