July 16, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Karan farko a tarihi an zabi mace a matsayin shugabar kungiyar ‘yan Jaridu a Jihar Kano

1 min read

Kungiyar ‘yan jaridu ta kasa ta ce, za ta ci gaba da kare mutuncin ‘yan Jaridu a kowanne mataki baga ya karfafa musu gwiwa don gudanar da ayyukan yadda ya kamata.

Shugaban kungiyar reshen Jihar Kano Abbas Ibrahim ne ya bayyana hakan yayin rantsar da sababbin shugabannin kungiyar ta tashar Freedom Radio a yau Laraba.

Kwamrade Abbas Ibrahim ya bukaci sabbain shugabannin da aka rantsar su zama masu aiki tukuru da kiyaye hakokin ma’aikata, yana mai cewa, da su kara kaimi wajen tabbatar aiwatar da nauyin da aka dora musu.

Da take jawabi, sabuwar shugabar kungiyar Kwamrade Hajiya Aisha Muhammad ‘Yalleman ta ce za suyi aiki tukuru, tare da kawo ci gaba a gidan Freedom Radio.

Jaridar Bustandaily ta rawaito an nada Hajiya Aisha Muhammad Yalleman a matsayin shugabar Kungiyar sai Abdullahi Isa a matsayin mataimakin shugabar kungiyar sai Muzammil Ibrahim Yakasai a matsayin Sakataren.

Sauran wadanda aka nada din akwai Abdulkarim Muhammad Abdulkarim a matsayin mataimakin Sakataren sai Adamu Sulaiman Muhammad a matsayin mai binciken kudi sai kuma Shamsiyya Farouk Bello a matsayin ma’aji.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *