June 13, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

A karo na Biyu ‘Yan Bindiga sun sace Dalibai masu zana WAEC

1 min read

Al-ummar garin Udawa da kewaye
sun ce hare-haren ‘yan bindiga ya hana su noma, yanzu
kuma ya na neman hana karatun boko. Yawan hare-
haren kuma ya sa mafi a kasarin mutane yin gudun
hijira.
Mazauna yankin shun shaidawa sashen Hausa na
Muryar Amurka cewa, akwai wasu mutane masu yawa
da ‘yan bindigar suka garkuwa da su a baya, amma
tsawon watanni har yanzu babu labarinsu duk da cewa
an biya kudaden fansa ma wasu.
Hare-haren ‘yan bindiga a wasu yankunan jihar
Kaduna, ya hana al’umomin yankunan sukuni. Amma
gwamnatin jahar Kaduna ta ce, ta na dukkan mai
yiwuwa dan kawo karshen wadannan hare-hare, a
cewar kwamishinan tsaro da karkokin cikin gida Malam
Samuel Aruwan.
Ayyukan ‘yan bindiga a yankunan karkara ya hana
manoma da dama zuwa gona, wanda wasu ke fargabar
zai iya haifar da karancin abinci a Najeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *