July 16, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

A shirye nake na sa hannu kan hukncin kisa ga wanda ya yi batanci ga Annabi

2 min read

Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya ce a shirye ya ke ya sanya hannun kan hukuncin kisan da wata babbar kotun musulunci ta yankewa wani matashi Yahaya Shariff Aminu sakamakon samunsa da laifin batanci ga Manzan Allah SAW, idan bai daukaka kara ba.

Gwamna Ganduje ya bayyana haka ne a yayin wata ganawa da malamai da kungiyar Lauyoyi ta Kano da kungiyar lauyoyi musulmi, da shugabnin hukumomin tsaro da ke jahar a yanmacin Alhamis din nan a dakin taro na Africa House da ke fadar Gwamnatin Kano.

A ranar Litinin 10 ga watan Agusta ne wata kotun shari’ar Musulunci ta yanke hukuncin rataya ga matashin, sai dai ta ce yana da damar daukaka ƙara.
Kotu a jihar Kano ta Yankewa wani matashi hukuncin kissa a bisa batanci ga Annabi SAW
Tun a watan Maris na 2020 Aminu Sharif, mazaunin unguwar Sharifai da ke ƙwaryar birnin Kano ya yi wata waƙa, wadda ya yi ɓatancin a cikinta.
Gwamnan na Kano Abdullahi Umar Ganduje ya ce ganin yadda alummar jahar da malamai ke ta matsin lamba kan ganin ya sa hannun a kan takardar hukuncin yasa ya bayyana matsayin sa, amma ya ce tunda kotu ta bai wa Yahya Shariff kwana talatin dole sai a jira har sai wa’adin ya cika.

Ganduje ya shidawa BBC cewa, “Idan wa’adin ya cika, wanda aka yankewa hukunci ya ki ya daukaka ƙara, kuma ba wata shida da muke da ita cewa ya daukaka ƙara, to gwamnan jihar Kano zai sa hannu.”
Gamayyar kungiyar Masoya Annabin Tsira ta bukaci Kisan Mai-Kano
Haka zalika gwamana Ganduje ya ce akwai buƙatar malamai su ci gaba da wayar da kan alumma dan gudun samun rikici tsakanin ƙungiyoyin addini da ake dasu a jahar, mussaman farwa wadanda Yahya Shariff din ya alakanta kan sa dashi.

Wani Babban Mutum a Nigeria zai gurfana gaban kotu saboda zagin Dan Jarida
Ƙungiyar lauyoyi ta jihar Kano ta ce ta yi na’am da wannan mataki da gwamnan na Kano ya dauka na yin aiki da doka, inda ta ce ya kamata al’umma su fahimci abun da doka ta ce kafin su yanke hukunci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *