June 13, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Dagacin Tudun Yola Ya karamta zancen dare tare da hana shaye-shayen miyagun kwayoyi a yankin

1 min read

Dagacin Unguwar ta Tudun Yola Malam Nasidi Hamisu ya ce daga yanzu zancen da Samari da ‘Yan Mata suke na tsakar dare haramun ne,kuma duk Wanda suka Kama za’ayi masa hukuncin da ya dashi.

Alhaji Nasidi Hamisu ya ce daukar wannan mataki ya biyo,bayan irin matsalolin tsaro da kwamitin unguwar suka dauka domin tsaftace yankin baki daya.

A cewar sa unguwar Tudun Yola unguwa ce Allah ya hada kan duk al’umma masu kudi talakawa da ‘yan kasuwa da kuma malamai da sauransu.
A dan haka ne, ya zama wajibi akan iyaye da su tashi tsaye domin kare tarbiyar ‘ya’yansu.

Da yake magana kan shaye-shayen miyagun kwayoyi, Dagacin ya ce daga yanzu,duk Wanda aka Kama da ta’ammali da kwaya ko dan gidan waye to tabbas sai ya fuskanci fishin kwamitin unguwar.

Ya kuma ce masu bada hayar Gidaje ko ta ammali da kasa,suma a yanzu dole su Fara sanar da mai unguwar da abin ya shafa,kafin bada haya ko siyar da fili.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *