June 13, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Dattawan Kano sun kai ƙararsa wajen Buhari

2 min read
Wata gamayyar kungiyoyi da ke rajin kare mutuncin mutanen Kano ta kai ƙarar Gwamnan jihar Abdullahi Ganduje ga Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari kan yunƙurinsa na ciyo bashi daga wani bankin China domin gina hanyar

Wata gamayyar kungiyoyi da ke rajin kare mutuncin mutanen Kano
ta kai ƙarar Gwamnan jihar Abdullahi Ganduje ga Shugaban Najeriya
Muhammadu Buhari kan yunƙurinsa na ciyo bashi daga wani bankin
China domin gina hanyar jirgin ƙasa.
Gamayyar kungiyoyi fiye da 15 ƙarƙashin inuwar Kano Forum ta
bayyana abin da ta kira katafaren bashin da gwamnatin Ganduje ke
son karɓowa domin gina kashin farko na hanyar jirgin ƙasa a birnin
Kano a matsayin abin da ba shi da amfani ganin manyan kalubalen
da ke gabanta.

Kungiyar ta yi zargin cewa Gwamna Ganduje zai ciyo bashin euro
miliyan 684, wato kimanin naira biliyan dari uku wanda suka ce sai
an shekara 50 gwamnatin ba ta gama biyan bashin ba.
Shugaban kungiyar Alhaji Bashir Othman Tofa ya ce: “Abu ne da
Want labarinGanduje ya maida martani kan zargin saida otel din Daula
kusan ba zai yiwu ba a ce jihar Kano ta ɗauki nauyin wani bashi fiye
da wanda aka riga aka jibga ma ta a baya.” A cewarsa, za su gurfanar da gwamnan a kotu idan ya zaɓi ci gaba
da shirin karɓo bashin.
“Wannan gamayyar za ta kuma bi duk wata hanyar da dokar ƙasa ta
samar domin hana gwamnatin ta Kano aiwatar da aikin samar da
hanyar jirgin ƙasa a Kano,” a cewar takardar da kungiyar ta fitar.
Kungiyar ta ce ciyo bashin zai jefa al’ummar Kano cikin kuncin
rayuwa tana mai cewa maimakon gina layin dogon, kamata ya yi
Wani labarinƳan Kwankwasiyya sun gurfanar da Gwamna Ganduje a gaban kuliya
gwamnati ta yi amfani da irin wannan bashi wajen kara ajujuwa da
samar da kayayyakin karatu, da kewaye makarantun jahar.
Sai dai Kwamishina watsa labarai na jihar ta Kano, Muhammad
Garba, ya ce ba za su fasa ciyo bashin ba.
Ya kara da cewa kungiyar ta tsirarun mutane ce kuma ba da yawun
al’ummar Kano take magana ba.
Rahotanni sun ce batun karbo bashin na cikin manyan abubuwan da
suka sanya Gwamna Ganduje ya sauke tsohon sarkin Kano daga kan
kujerar mulki sakamakon sukar da ya yi masa a kan shirin.
A kwanakin baya ‘yan kungiyar Kwankwasiyya da ke goyon bayan
tsohon gwamnan Kano Raib’u Kwankwaso, sun kai kai karar
gwamanan na Kano abdullahi Umar Ganduje kotu inda suka nemi ta
dakatar da shi ciy bashin na naira biliyan dari uku da

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *