June 13, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Ko menene Nagarta a musulunci-Zainab Jafar Mahmud Adam

2 min read

Addinin musulunci addini ne mai tsari da ƙa’ida da sanya kowanne abu a gurbinsa da ya kamata. Ya shar’anta cewa shuwagabanni su ke da alhakin tantance abinda ya shafi ganin wata ko rashin ganinshi tare da shelantawa al’umma hakan, wannan nauyi ne da yake kansu wanda wajibi ne su ji tsoron Allah wajen saukeshi. Kamar yadda mu kuma sauran jama’a abinda yake kan mu shine biyayya ba tare da kawo hayaniya ko cece-kuce ba, domin hakan laifi ne.

Amma abin takaici duk san da kamawa ko mutuwar wani wata yazo da yake da alaƙa da wata ibada sai mutanenmu sun yi ta mitar an gani ko ba a gani ba, kai ka ce mu muke da wannan alhakin a ɗaiɗaikunmu. Mu ji tsoron ALLAH mu daina haifar da rudani a cikin al’umma, in har hukumomi sun sanar da shigar wata ko mutuwarshi wajibinmu shi ne mu bi, fatanmu dai har kullum shine Allah ya taimaki shuwagabannin mu akan dukkanin abinda yake daidai amin.

Fadar Mai alfarma Sarkin Musulmin Nigeria ta bada sanarwar Juma’a da ta gabata 21st August 2020 ita ce 1st Muharram 1442H, dan haka Asabar 29th August 2020 ita ce za ta yi daidai da 9th Muharram 1442H, Lahadi da za ta biyo bayanta kuma 10th Muharram, ga mai niyyar azumtar TASU’A DA ASHURA a Nigeria wannan su ne ranakun da zai azumta. Mu sani ba a amfani da lissafin ganin watan wata ƙasar da ba a cikinta mutum yake zaune ba, abinda mahukuntan ƙasar da kake suka sanar shine yake wajibi kayi aiki da shi.

‘Yan uwa mu ji tsoron Allah mu daina kawo ruɗu a cikin al’umma, Allah ka shiryar da mu zuwa ga aikata daidai ka kuma amshi ibadunmu amin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *