July 18, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Malamin Islamiyya a Jihar Kano ya ce ko Gwamnati zata yanka shi sai ya bude Makaranta

1 min read

Malamin mai suna Ahmad Inuwa ya ce bazai juri, rainin hankali ba,domin a baya sun yi shiru kasancwwar girmama shugaba wajibine,amma yanzu lokaci yayi da zai bujirewa wannan doka.

A cewar sa annobar corona ta kare a jihar kuma dalilinta ne ya sanya kulle makarantun.
Ya kuma ce,tin a watan Maris din shekara 2020,corona ta kare a jihar Kano.

Haka zalika malamin ya ce babu wani shugaba ko shugaban NCDC c ko gwamna ko Jami’an tsaro da yake tsoron yazo ya kamashi,domin ya shirya,kuma ko me za’ayi masa sai ya bude mskarantar sa.

Malaman islamiyya a jihar Kano, na ta kira da gwamnatin jihar Kano kan ta bude Makarantun,sai dai kuma a tabakin Shugaban hukumar Lura da tsangayun islamiyya Islsmiyya Gwani Yahuza Gwani Dan Zarga ya ce Gwamnatin na shirin duba yuhuwar budewa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *