Wani Babban Mutum a Nigeria zai gurfana gaban kotu saboda zagin Dan Jarida
1 min read
A cikin wani sakon da Fani-
Kayode ya wallafa a shafinsa na Twitter ya ce, “Na
janye kalmomin da na yi amfani da su kan wani dan
jarida. Ina da abokai ‘yan jarida da dama da
kalmomina suka fusatar. Na yi nadama sosai.”
Sai dai tsohon Ministan ya musanta zarge-zargen da ke
cewa zai sa a ci zarafin dan jaridar na Daily Trust.
“Na yi imanin cewa ba abinda aka yi wa dan jaridar
kuma ni ban aika kowa ya ci zarafinsa ba. Duk wanda
ya ce an yi hakan to karya yake yi.”
A cewar Fani-Kayode, ya yi shekara 30 yana aiki da
‘yan jarida kuma yana daga cikin wadanda suka yi
fafutukar samun ‘yancin fadin albarkacin baki saboda
haka ba zai taba cin zarafin kowane dan jarida ba.
Hakan dai duk na faruwa bayan da ya sha matukar
suka daga ‘yan Najeriya da dama kan shafukan sada
zumunta sakamakon abinda ya yi.
An yi ta yada faifen bidiyon faruwar lamarin kan
intanet inda aka ga yadda ya za-zage dan jaridar yayin
da shi kuma ya rinka ba tsohon ministan hakuri.