June 23, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Ɗalibai fiye da 40 da ke rubata WAEC sun kamu da cutar da corona

2 min read

Ɗalibai fiye da arba’in da ke rubuta jarrabawar kammala sakandare
ta WAEC sun kamu da cutar korona a Najeriya – akasari a jihohin
Gombe da Bayelsa.
Hukumomi a jihar Bayelsa da ke kudancin ƙasar sun tabbatar da
kamuwar aƙalla ɗalibai ashirin.
A Akwa Ibom kuma rahotanni na cewa ɗalibi daya ya kamu, yayin da
a jihar Gombe da ke arewacin kasar ɗalibai ashirin suka kamu.
Kwamishinan Ilimi na Gombe, Dr Habu Dahiru, ya shaida wa BBC
cewa an gudanar da gwaje-gwaje ga ɗalibai da malamai a
makarantun kwana guda ashirin da ke jihar, kuma aka samu ɗalibai
ashirin dauke da cutar a makarantu shida kawo yanzu.


”Ɗalibai sama da dubu muka yi wa wannan gwaji, kuma babu wanda
za a je ba zai rubuta wannan jarrabawa ba saboda ya kamu da cutar.
A karo na Biyu ‘Yan Bindiga sun sace Dalibai masu zana WAEC
Ɗaliban sun cigaba da daukan jarrabawar a gefe da kowacce
makaranta ta ware domin killace duk wani ɗalibi da aka samu dauke
da cutar.”
Dr Habu ya kuma kara da cewa akasarin ɗaliban basu nuna wata
alamar cutar ba ko shiga yanayi mai tsanani, sannan akwai wayanda
suka warke ma.
Daliban Najeriya sama da 100 aka hallaka
A makon jiya ne dai ɗalibai fiye da muliyan daya da dubu dari biyar
suka fara rubuta jarrabawar ta WAEC bayan da aka jinkirta jarrabawar
saboda tsoron yaduwar cutar ta korona.
Jarrabar WAEC tana da muhimmanci domin ita ke shirya yara samun
damar shiga Jami’a da aikin yi.
Ba dole sai dalibai sun nemi aikin gwamnati ba-kungiyar daliban Yusuf Maitama Sule
Akwai dubban yara da ke irin wannan jarrabar a ƙasashe irin su
Ghana da Saliyo da Gambia.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *