June 13, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Ba zamu amince da korar Ma’aikata barkatai da sunan annobar Coronavirus ba-NLC

1 min read

Kungiyar kwadago ta kasa NLC ta ce baza ta lamunci fakewa da wasu gwamnatoci da sauran ma’aikatu ke yi ba, bayan da kasar nan ta fada cikin jerin kasashen da annobar corona ta shafa wajen sallamar ma’aikatan tare da danni musu hakkokin su.
Kungiyar Kwadago a Nigeria zata gudanar da zanga-zanga.
Shugaban kungiyar Ayuba Wabba ne ya bayyana hakan lokacin da yake zantawa da manema labarai jiya Laraba a birnin tarayya Abuja.

Ya ce tuni ma’aikata suka zargi yadda ake fakewa da annobar corona ana danne musu hakkokin su.
Ayuba Wabba yace a don haka kungiyar kwadago zata yi duk mai yiwuwa wajen magance wannan matsala musamman ta dannewa ma’aikata hakki, yana mai cewa aikin kungiyar ne ta sharewa ‘ya’yanta hawaye musamman na kalubalen da suke fuskanta a guraren ayyukan su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *