July 12, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Dokar tsaftar Muhalli babu dalibai masu zana jarabawar WAEC

1 min read

Gwamnatin jihar Kano ta sahalewa Daliban dake rubuta Jarabawar
kammala Sakandire ta yammacin Afrika WAEC fita a gobe asabar
duk da cewa za a gudanar tsafatar muhalli a fadin jihar Kano.
A karo na Biyu ‘Yan Bindiga sun sace Dalibai masu zana WAEC
Kwamishinan muhalli na jihar Kano Dakta Kabiru Ibrahim Getso ne
ya bayyana hakan a yau lokacin da yake jawabi bayan kammala
gudanar da duban tsaftar muhalli na kasuwanni da hukumomin
gwamnati har ma tashoshin mota da ake gudanarwa a karshen
kowanne wata.
An sace Dalibai Mata Masu zana Jarabawar WAEC a jiya
Ya ce, ma’aikatar muhalli ta samar da wata shaidar da za a rabawa
jami’an da ke sintirin raba kayan jarrabawar da kuma malaman da ke
kula da rubuta jarrabawar ta yadda za su nuna a matsayin shaida a
gobe don basu damar zuwa cibiyoyin rubuta jarrabawar.

Dakta Getso, ya kuma ce dalibai kuwa kayan makarantar su da kuma
katin jarrabawar su zai zamo shaidar da za su fita a gobe asabar
don rubuta jarrabawar.

Sai dai ya bukaci wadanda aka sahalewa dokar da su yi amfani da
lokacin wajen isa guraren da wuri don baiwa jami’an tsaftar muhalli
damar gudanar da ayyukan su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *