June 23, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Rundunar Sojin Nigeria ta tarwatsa sansanin ‘yan Darussalam

1 min read

Rundunar sojin Najeriya ta ce dakarunta sun tarwatsa wani sansanin masu tayar-da-kayar-baya da aka fi sani da Darussalam a yankin Uttu da kewaye da ke karamar hukumar Toto a jihar Nasarawa.
Sojoji uku sunyi wasan kura da ‘yan karota,a yau Laraba.
Rundunar ta ce dakarunta sun cimma sansanin `yan kungiyar ne tare da hadin gwiwar sauran jami`an tsaro, bayan sun tattara muhimman bayanai a kan maboyarsu.


Yayin harin rundunar ta ce jami’anta sun yi arangama da mayakan kungiyar wadanda daga bisani suka tsere, suka bar matansu, wadanda suka mika-wuya ga sojojin. Kakakin cibiyar samar da bayanai a kan arangamar da sojojin Najeriya ke yi a sassan kasar Kwamanda Abdussalam Sani, ya shaida wa BBC cewa mutum fiye da dari hudu ne suka mika wuya, yawanci mata da kananan yara.
Sojojin Najeriya sun tarwatsa ‘yan fashi a Kaduna.
Ya ce, ”An samu wata cibiya da suke kera abubuwan fashewa, an kuma gano manyan bindigu guda shida, da buhun taki da suke amfani da shi da gurnet-gurnet”.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *