July 12, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Sama da Naira Miliyan 30 Manoma za su yi a sara -hukumar karfar korafe-korafe ta Kano

2 min read

Wasu Manoma dake karamar hukumar Tudun Wada sun bukaci Gwamnatin jihar Kano data shiga tsakanin su da hukumar karbar korafe-korafe da yaki da cin hanci da rashawa bisa yadda ta hana su shiga gobakin su.
Gwamnan Sokoto Aminu Tambuwal ya umarci manoma su koma bakin ayyukansu.
A cewar manoman sun mallaki gonakin sune, ta hannun karamar hukumar Tudun Wada,kuma tini suka yi noman Shinkafa na sama sa miliyan 30 a gonakin,amma lokaci guda an hana su shiga gonakin nasu

Manoman Wanda suka ce a yanzu haka sun narka kudade sama da naira miliyan 30 wajen shuka shinkafar, kuma ma an kusa girbe ta, amma an hana su shiga gonakin nasu wanda hakan zai haddasa musu mummunar hasara kasancewar shinkafar zata lalace.
An kashe manoma 20 a wani kazamin hari.
Da yake maganar gonakin a hannun hukumar sauraren korafe-korafan ta jihar Kano yake, hakan ne ya sanya muka tuntube shugaban hukumar Barr Muhyi Magani Rimin Gado domin jin ta bakin sa kan wannan batu.
Ana zargin dagacin Yalwa da cinyewa wasu manoma gonakansu.
Barr Muhyi ya kuma ce kasancewar wasu mutane na siyar da kayan gwamnati ba bisa ka’ida ba,inda ya ce duk manomin da suka samu a gonar sai sun gurfanar da shi gaban kotu.

Abin tambayar shi ne,wadannan manoma sun noma shinkafa ta sama da Miliyan 30,Wanda kadan ya rage ta gama girma yanzu rashin barin manoman ya sanya shinkafar za’ayi a sarar ta.

Akwai dai bukatar a kalli irin makudan kudin da manoman suka narka wajen aikin shinkafar don samun maslaha da kaucewa tashin tarzoma.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *