July 18, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Shugaban Kasar Nigeria ya nada manyan Jami’ai da hukumomi Tara a Ma’aikatar yada Labarai

1 min read

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada wasu manyan jami’ai a hukumomi tara karkashin ma’aikatar yada labarai da raya al’adu.

Hakan na cikin sanarwar da ministan yada labarai da raya al’adu Alhaji Lai Muhammad mai dauke da amincewar shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa Farfesa Ibrahim Gambari wadda mai baiwa shugaban kasa shawara na musamman Mr Segun Adeyemi ya sanyawa hannu.
Dattawan Kano sun kai ƙararsa wajen Buhari
Sanarwar ta ce, an nada Mr Buki Ponle a matsayin manajan daraktan kamfanin dillancin labarai ta kasa NAN yayin da Alhaji Nura Sani Kangiwa aka nada shi a matsayin darakta janar na cibiyar nazarin yawon bude ido da karbar baki.
Mai dakin shugaban Kasar Nigeria Aisha Buhari ta magantu bisa matsalar data samu a jiya
Sauran su ne : Mr Ndubuisi Nwosu a matsayin babban darakta a majalisar ‘yan jarida ta kasa sai Mr Olalekan Fadolapo a matsayin magatakarda a hukumar Tallace tallace ta kasa APCON da dai sauran su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *