June 13, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

An Nada Shugabannin Hukumar Kula Da Gajiyayyu Ta Najeriya

2 min read

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya amince da nada
shugabannin sabuwar hukumar kula da masu larura ta
musamman ta kasar.
An kafa sabuwar hukumar ta kula
da masu nakasa da ke bukatar kulawa ta musamman
ne bisa tanadin dokar yaki da kyamar masu nakasa ta
shekara 2019.
Tsohon dan majalisar wakilai daga Jihar Kebbi Husseini
Suleiman Kangiwa shi ne sabon shugaban hukumar, a
yayin da aka nada Abba Ibrahim daga Arewa Maso
Gabas a matsayin Sakatare.
Dokar tsaftar Muhalli babu dalibai masu zana jarabawar WAEC
Wannan hukumar na da manufar kula da masu larura
ta musamman da yawan su ya kai miliyan 25 a
Najeriya, ta hanyar samar da karin kashi 5 cikin dari
na aiyukan yi, da kuma ba su kulawa ta musamman
akan batutuwan da suka dame su a dukan fanoni na
rayuwa da kiwon lafiya da kuma harkokin walwalarsu
da nufin share masu hawaye.
Daya daga cikin shugabanin kungiyoyin masu larurar
na kasa sakamakoni cutar shan inna Misbahu Lawal
Didi ya ce yanzu ne masu fama da nakasa za su fara
samun damar shiga a dama da su a harkokin mulki a
Najeriya.
Misbahu ya yaba da wanan kokari da Gwamnati ta yi,
wanda ya ce dama sun dade suna jiran irinsa, domin
baiwa mutanensu damar ba da ta su gudummuwa a
harkokin cigaban kasa, wanda hukumar za ta taimaka
masu gaya wajen cimma wannan burin.
Abin da ya dauki hankali a yanzu shi ne kulawar da
mata masu nakasa za su samu, la’akari da irin rawar da
suka taka a lokacin gwagwarmayar kafa wanan
hukuma.
Shugabar mata masu larura a kasar, Rabi Yusuf
Gezawa, ta ce za su ci gaba da fafutukar tabbatar da ba
a bar mata a baya ba a wajen cin gajiyar hukumar.
Rabi Gezawa ta ce sun fito kwansu da kwarkwata a
kokarin ganin an samu Hukumar ta kula da masu
bukata ta musamman duk da cewa suna da aure inda
ta yi rokon kar maza su danne su a yanzu da kwaliya ta
biya kudin sabulu.
Mashawarci na musamman ga shugaban kasa a
lamurran masu larura ta musamman Shehu Garba, ya
shawarci ‘yanuwansa da su sakawa wannan kokari na
Gwamnati ta hanyar yin addu’o’i da fatan alheri.
Sarkin da ba’a Sanar da Mutuwarsa a hukumance sai bayan ya Mutu
Ya ce wannan dama ce da gwamnatin ta sama musu na
more romon damokradiya tunda ta nuna masu kauna
tareda ba su kafa na samun hakkokin su a cikin sauki
ta hanyar hukuma da za ta kula da lamuran su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *