July 12, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Gwamnatin Nigeria ta ce zata Bawa Matasan Npower gurbin ayyukan yi

1 min read

Gwamnatin tarayya ta ce shirye-shirye sun yi nisa wajen ganin an
sanya matasan da suka ci gajiyar shirin nan na Npower cikin wasu
tsare-tsare na hukumomin gwamnatin tarayya.

Ministar kula da harkokin jinkai dakile abkuwar ibtila’I da kuma ci
gaban al’umma, Hajiya Sadiya Umar Faruk ce ta bayyana hakan ta
cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun mai magana da
yawunta, Nneka Anibeze.

Sanarwar ta kuma bukaci matasan da suka ci gajiyar shirin na
NPOWER wadanda aka yayesu da su ci gaba da hakuri domin
gwamnati tana iya kokarinta wajen ganin an samar musu mafita.
Sama da matasa Miliyan biyar suka nemi shiga shirin Npower
Za’a kafe sunayen wadanda suka samu nasarar shiga shirin Npower
A cewar sanarwar dai ma’aikatar ta kuma bukaci dukkan nin manyan
jami’an da ke kula da shirin na NPOWER A matakan jihohi da su mika
da sunayen matasan da su kaci gajiyar shirin a jihohinsu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *