June 13, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Sarkin da ba’a Sanar da Mutuwarsa a hukumance sai bayan ya Mutu

5 min read

AttahASALIN HOTON,FACEBOOK/IDAKWO MICHAEL AMEH OBONI
Duk da cewa labarin mutuwar Attah na masarautar Igala Michael Ameh Oboni II ya baza duniya, to har yanzu a hukumance ba a sanar da mutuwar sarkin ba.

A tsarin al’ada irin ta Masarautar Igala da ke jihar Kogi a arewa ta tsakiyar Najeriya, ba a sanar da mutuwar sarkin daular har sai bayan wasu kwanaki.

Amma BBC ta samu bayanai da ke tabbatar da mutuwar tasa daga wasu majiyoyi masu ƙarfi na gwamnatin jihar ta Kogi.

A ranar Alhamis ne rahotanni suka fara fita na labarin mutuwar Michael Ameh Oboni II, Sarkin Igala wanda ake kira Attah na Igala.

Igala na ɗaya daga cikin manyan ƙabilun yankin arewa ta tsakiyar NajeriyavvSashen BBC Pidgin ya gano cewa Mai Martaba Michael Ameh Oboni II ya mutu ne a wani asibiti a Abuja.
Shugaban Kasar Nigeria ya nada manyan Jami’ai da hukumomi Tara a Ma’aikatar yada Labarai
Amma ba a san irin cutar da ta zama ajalinsa ba.

Tsohon mai bai wa gwamnan Kogi shawara kan yaɗa labarai Gbenga Olorunpomi ma ya tabbatar da labarain mutuwar a shafinsa na Tuwita.

Wane ne Mai Martaba Michael Ameh Oboni II na Masarautar Igala?
Michael Ameh Oboni II ya kasance a gadon sarautar Igala tsawon shekara bakwai.

An haifi Yarima Idakwo Michael Ameh Oboni a shekarar 1948.

Ya shiga rundunar sojin saman Najeriya a shekarar 1968 sannan ya bar aiki a shekarar 1974 bisa raɗin kansa.
Five ways a smartphone can help your health
Yarima Idakwo ya yi aiki na ɗan lokaci a Ma’aikatar Filaye a tsohuwar jihar Kwara da ke arewa ta tsakiyar Najeriya a matsayin jami’i mai kula da filaye daga 1974 zuwa 1975.

ASALIN HOTON,FACEBOOK/IDAKWO MICHAEL AMEH OBONI
Daga baya ya yi murabus a shekarar 1975 ya koma Makarantar Kaduna Polytechnic a shekarar 1976 don karantar fannin Kula da Rukunin Gidaje inda ya kammala a shekarar 1980.

A shekarar 1981 ya samu aiki da Ma’aikatar Kula da Babban Birnin Tarayya Abuja FCDA, inda ya yi ritaya a shekarar 2006 a matsayin mataimakin darakta.

Michael Ameh Oboni II shi kaɗai ne sarkin Igala da ya zauna da mace ɗaya a tarihi.

Shi ne Sarkin Igala na 27 a jerin sarakunan daular.

Tsohon gwamnan Kogi Idris Wada ne ya amince da naɗinsa a matsayin sabon Attah Igala a shekarar 2013.

Yadda sarautar Attah ta zama mai girma a daular
Da farko dai duk wani Attah shi ne jagoran addini na wannan ƙabilar. Attah na Igala yana taka rawa biyu, da zamantowarsa jagoran addini da kuma sarkin Daular Igala.

Girman masarautarsa ta fara daga kudanci zuwa arewacin ƙasar; daga gaɓar Kogin Neja zuwa yankin kudu maso gabas.

Baya ga haka, Attah na da ƙarfin iko kan sauran sarakunan yankinsa da kuma albarkatun ƙasar da ke masarautarsa.

Kamar sauran manyan sarakuna, shi ma Attah akwai abubuwan da yake iya yin su da akwai kuma waɗanda ba ya iyawa.

Akwai abubuwa da dama da Attah na Igala ba zai iya yi ba
Attah ba ya cin abinci ko yin rawa a gaban mutane
Ba ya shan hannu da kowace mace
A al’adance Attah ba zai ɗauki kowane jaririn da bai kai wata uku ba
Attah ba ya hawa kwale-kwale
Ba ya kallon gawa da idonsa
Kuma babban aikinsa shi ne ya kare al’ummar Masarautar Igala.
Me zai faru bayan mutuwarsa?
Akwai gidaje huɗu na gidan sarautar Igala – da gidan Ocholi da gidan Aju Akwu da gidan Aju Amacho da gidan Aju Akogwu amma dukkansu sun fito daga tsatson Ayegba.

Waɗannan gidajen duk suna karɓa-karɓa na sarautar daular.

A wata tsohuwar hira da ya yi da Punch, Attah Igala Ameh Oboni ya fayyace yadda za su zaɓi sabon sarki bayan mutuwar wanda ke kan gadon.

“Bayan iyalan da sabon sarki zai fito daga gidansu sun yanke hukunci kan wanda suka zaɓa, sai a ce musu su je su gana da wani babba a masarautar da ake kira Etemayi.

Etemayi zai haɗu da Achadu (mutum na gaba da zai zama Attah) sai ya ce masa kai ne sarki mai jiran gado.

Sai a duba shi a ga ko yana da cikakkiyar lafiya ba tare da wata naƙasa ba, sannan za a duba a ga ko yana da in’ina.

Duk mutumin da yake in’ina ba zai zama Attah ba. Sannan zai kasance mai matsakaicin tsayi, idan duk bai cike waɗannan sharuɗɗan ba to sai a cewa gidan su sake kawo wani.

Bayan wannan, sai shi wanda aka zaɓa mai jiran gadon ya yi tafiyar mil 16 da ƙafa zuwa Ugwolawo, inda zai kwana ana ya gobe za a naɗa shi.

Idan aka fara bikin naɗin sarautar a garin Idah, sai a tafi da wasu malaman ƙabilar zuwa maƙabarta don su yi wasu abubuwa na al’ada don gano yadda mulkin sabon sarkin zai kasance.

Idan duk a ƙarshe suka yarda cewa zai kawowa masarutar zaman lafiya sai su tafi su naɗa shi washe gari da safe.
Wane ne Mai Martaba Michael Ameh Oboni II na Masarautar Igala?
Michael Ameh Oboni II ya kasance a gadon sarautar Igala tsawon shekara bakwai.

An haifi Yarima Idakwo Michael Ameh Oboni a shekarar 1948.

Ya shiga rundunar sojin saman Najeriya a shekarar 1968 sannan ya bar aiki a shekarar 1974 bisa raɗin kansa.

Yarima Idakwo ya yi aiki na ɗan lokaci a Ma’aikatar Filaye a tsohuwar jihar Kwara da ke arewa ta tsakiyar Najeriya a matsayin jami’i mai kula da filaye daga 1974 zuwa 1975.

ASALIN HOTON,FACEBOOK/IDAKWO MICHAEL AMEH OBONI
Daga baya ya yi murabus a shekarar 1975 ya koma Makarantar Kaduna Polytechnic a shekarar 1976 don karantar fannin Kula da Rukunin Gidaje inda ya kammala a shekarar 1980.
Ɗalibai fiye da 40 da ke rubata WAEC sun kamu da cutar da corona
A shekarar 1981 ya samu aiki da Ma’aikatar Kula da Babban Birnin Tarayya Abuja FCDA, inda ya yi ritaya a shekarar 2006 a matsayin mataimakin darakta.

Michael Ameh Oboni II shi kaɗai ne sarkin Igala da ya zauna da mace ɗaya a tarihi.

Shi ne Sarkin Igala na 27 a jerin sarakunan daular.

Tsohon gwamnan Kogi Idris Wada ne ya amince da naɗinsa a matsayin sabon Attah Igala a shekarar 2013.
Gwamnatin Nigeria ta ce zata Bawa Matasan Npower gurbin ayyukan yi
Yadda sarautar Attah ta zama mai girma a daular
Da farko dai duk wani Attah shi ne jagoran addini na wannan ƙabilar. Attah na Igala yana taka rawa biyu, da zamantowarsa jagoran addini da kuma sarkin Daular Igala.
Ɗalibai fiye da 40 da ke rubata WAEC sun kamu da cutar da corona
Girman masarautarsa ta fara daga kudanci zuwa arewacin ƙasar; daga gaɓar Kogin Neja zuwa yankin kudu maso gabas.

Baya ga haka, Attah na da ƙarfin iko kan sauran sarakunan yankinsa da kuma albarkatun ƙasar da ke masarautarsa.

Kamar sauran manyan sarakuna, shi ma Attah akwai abubuwan da yake iya yin su da akwai kuma waɗanda ba ya iyawa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *