July 12, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Zamu tsaya takarar shugaban Kasa a Nigeria Allah ne yake bada Mulki ba Mutum-Sunusi Lamido

3 min read

Muhammadu Sanusi na biyu
wanda ke ganawa da al’umma daban-daban a Kaduna
bayan kwashe dogon lokaci a jahar Ikko , ya bayyana
cewa, shi ne jika na farko a tarihin masarautar Kano da
Allah Ya bashi sarauta. Yace “in dai an yarda cewa,
Allah ba ya zalunci, to duk abinda ya same ka idan dai
baka zalunci gwamnati ko ‘yan uwanka ko kuma
al’umma ba, ba kuma za a iya cewa ga abinda ka yi ba,
sai ka godewa Allah ”
Tsohon sarkin ya ce abinda ya sa bai yi magana ba
shine sanin cewa, “daukaka ake nema, ba mulki ba.”

Yace ” Allah ne ke bada mulki ga wanda Ya ga dama,
saboda haka idan Ya bada mulki sai a gode masa . ”
Tsohon sarkin ya bayyana godiya da kaunar da yace
al’umar Kano ta nuna mashi, ya kuma ce ‘yana tare da
su’.
Tsohon Sarkin Kano Sunusi Lamido zai tsaya takarar shugaban Kasar Nigeria-2023
Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II (Hagu) Ya Na Mika
Kyauta Ga Muhammed Babangida, Wanda Ya Lashe
Wasan Dawakai a Karakashin Kungiyar MTN a Lokacin
Gasar Lashe Kofin Hassan E. Hadeja a Kaduna a Ranar
4 ga Watan Nuwamba, 2015
Muhammadu Sanusi na biyu ya ce idan ya yi fushi
sabili da an cire shi daga sarauta ya yi wa Allah butulci,
saboda yana iya hana shi mulki tun da farko yana
kuma iya daukar ranshi a maimakon sauke shi daga
mulki.
LABARI DA DUMI DUMI An nada tsohon Sarkin Kano Khalifan Tijjani na Afrika.
Yace kasancewa Allah Ya bar shi da rai da lafiya
da kuma iyalinshi , ya isa abin godiya.
Tsohon sarkin Kanon ya kuma ce, sarauta rai ne da ita,
saboda haka mutum baya wuce ranar da Allah Ya dibar
mashi, amma ba domin ikon gwamnati ba. Yace a cikin
shekaru dari biyu, an yi mutane dubbai amma Allah
bai basu mulki ba har da mahaifinshi da yake dan
Sarki.
Sarkin Kano yayi nade-nade na farko tin bayan hawansa kan mulki.
.Ya bayyana cewa ya sauke hakin al’umma dake
wuyansa iyaka iyawarsa a cikin shekaru shida da ya yi
yana mulki. Yana mai cewa…
“Zuri’ar Dabo mutum nawa ne, a cikin mutum dubban
nan cikin shekara dari biyu, ni ne na goma sha biyu kadai
a cikin dubbai da Allah Ya ba. Bai ba mahaifina ba kuma
dan sarki ne. Bai taba ba wani jika ba, ni Ya fara baiwa
wani jika …to banda ka gode masa har ka mutu , me za ka
ce wa Allah?”
A cikin jawabansu, malaman Sunnan karkashin
jagorancin Sheik Adam Koki da Sheik Aminu Ibrahim
Daurawa, sun bayyana cewa, sarauta da matsayi da
kuma dajarar kujerar Sarauta tana bin mutum ne , ba
kujera ba, suka kuma bayyana cewa al’ummar jihar
Kano tana matukar kaunar Muhammadu Sanusi na
biyu tare da yi mashi fatar alheri.
Magoya bayan tsohon Sarkin sun hakikanta cewa, an
sauke shi daga sarauta ne sabili da rashin goyon bayan
sake zaben Ganduje bara, zargin da gwamnatin jihar
Kano ta musanta.

Gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje ya sauke
Muhammadu Sanusi daga sarauta ranar tara ga watan
Maris na shekara ta dubu biyu da ishirin bisa zargin
cewa tsohon sarkin ya sabawa wani sashi na dokokin
masarautar Kano.
Ba zamu amince da korar Ma’aikata barkatai da sunan annobar Coronavirus ba-NLC
An dai nada Muhammadu Sanusi na biyu a matsayin
Sarkin Kano ne a ranar takwas ga watan Yunin
shekarar 2014, bayan rasuwar kawunsa Ado Bayero.

Kafin hawanshi kujerar sarauta r , ya yi aiki a matsayin
shugaban babban bankin Najeriya daga shekarar 2009
zuwa 2014 karkashin mulkin tsohon shugaban Najeriya,

Goodluck Jonathan.
Muhammadu Sanusi na biyu yana yawan magana kan
batutuwa da suka shafi harkokin mulki, tattalin arziki
da rayuwar al’umma da ya hada da batun aure da
zaman gida.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *