An karrama gwarzon karen da ya ceto rayukan sojoji a Afghanistan
2 min read
Wani karen sojoji da ya ratsa cikin harbin harsasai da abokan gaba
ke yi domin ya ceto rayukan sojojin Birtaniya da ke yaƙi da al Qaeda
a Afghanistan ya sami lambar yabo mai darajar ta Gicciyen Victoria
(Victoria Cross).
Yayin wani hari, karen mai suna Kuno ya kai wa wani ɗan bindiga
hari, kuma an harbe shi a kafafuwansa biyu na baya.
Bayan ya rasa kafarsa ɗaya ta baya a sandiyyar harbin, Kuno ya
zama karen sojojin Birtaniya na farko da aka saka wa kafar roba ta
musamman.
Za a kuma karrama karen mai shekara huɗu da haihuwa da lambar
yabo ta Dickin daga gidauniyar dabbobi ta PDSA.
A hali yanzu an yi wa Kuno ritaya daga aiki – aikin da ya haɗa da gano
bama-bamai da makamai da kuma kassara abokan gaba – kuma za a
karrama shi a wani taro da za a gudanar ta intanet a watan
Nuwamba.
Tun da farko dai an tura Kuno da mai kula da shi wani sansani domin
tallafa wa ayyukan wata runduna da suka kai wani hari cikin dare kan
mayakan al Qaeda a Afghanistan a bara inda aka kai musu hari.
Dakarun da yake tare da su sun kasa motsawa saboda yawan harbin
da mayakan al Qaedan ke yi mu su.
An saki Kuno domin ya warware matsalar, kuma ba tare da wata-
wata ba, ya ratsa cikin ruwan harsasan da abokan gaban ke harbawa
yana sanye da wani tabarau mai taimakawa gani cikin duhu. Ya sami
nasarar kayar da ɗan bindigar zuwa ƙasa, matakin da ya kawo
ƙarshen harin.
Amma yayin harin ne aka harbe shi a kafafuunsa biyu na baya kuma
mai kula da shi ya sanya ma sa magani kuma ma’aikatan jinya sun
kula da shi cikin helikwaftan da ya mayar da su sansaninsu. Daga
baya an mayar da shi Birtaniya domin yi masa magani.
A can ne aka gano yawan raunukan da Kuno ya samu, kuma likitocin
dabbobi sun yanke wani bangare na kafarsa ɗaya ta baya.
Bayan wannan lkacin ne aka yi masa aiki da ya hada da sake gina
kafar tasa.
Cikin watanni sai aka sanya ma sa wata kafar roba ta musamman da
ta maye gurbin kafar tasa ta baya da aka yanke.
Babban shugaban gidauniyar PDSA Jan McLoughlin sun ce jaruntar
da Kuno ya nuna ce ta sa suka karrama shi da lambar yabo ta Dickin.
Wannan babbar lambar yabo ce da aka fara karrama dabbobi da ita
tun 1943, kuma wannan ce lambar yabo tda tafi girma da ke ba
dabbobin da ke ayyuka a fagen yaki.
Kuno ne kare na 72 da za a karrama da wannan lambar yabon, cikin
karnuka 34, da tantabaru 32 da dawaki huɗu da mage ɗaya.ui