July 16, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Labari da dumi duminsa An Ci Gaba Da Zanga-zanga

1 min read

Kimanin mutane 1,000 suka yi
maci a Kenosha ta jihar Wisconsin a ranar Assabar, a
karkashin jagorancin iyalan bakar fatan da ‘yan sanda
suka harba, a fafutukar neman kai karshen cin zarafin
da ‘yan sanda ke yi a birnin na tsakiyar yammacin
Amurka.


Shugaba Donald Trump zai ziyarci birnin a ranar
Talata, domin tattaunawa da jami’an hukumomin tsaro
da kuma kiyasin al’amarin, a cewar wani jami’in fadar
Shugaban kasa ta White House.
Jacob Blake Sr.

wanda sashen hagu na jikin dan sa ya
mutu sakamakon harbin da wani dan sanda farar fata
ya yi masa a makon jiya, ya yi kira ga masu zanga-
zangar da su yi ta cikin lumana, kuma su kaucewa
tashin hankali.Dangin Blake da ‘yan fafutuka ne suka shirya zanga-
zangar, a yayin da dakarun tsaron kasa suke gefensu a
cikin shirin ko-ta-kwana, domin hana barkewar tashin
hankali da ya soma aukuwa a Kenosha a farkon makon
sakamakon harbin da aka yi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *