July 16, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

An Kashe Mutum guda a yayin wata Zanga Zanga safiyar Litinin

1 min read

Hukumomi sun ce an bindige
wani mutum har lahira da daren jiya Asabar garin
Portland na jahar Oregon, yayin da wata arangama ta
barke tsakanin wasu magoya bayan Shugaba Donald
Trump masu jeren gwanon motoci, da masu zanga-
zanga kan wariyar da su ke zargin ‘yan sanda na wa
bakaken fata, da aka fi sani da Black Lives Matter, a
cewar ‘yan sanda.
Masu zanga-zanga sun cinnawa ofishin majalisa wuta.
Zuwa yanzu, bayanai na nuna cewa wanda aka harba
din farar fata ne. Ba a tabbatar ko harbin na da nasaba,
kai tsaye, da fadan da ya barke, bayan da masu zanga-
zangar su ka tinkari tawagar motoci wajen 600, na
magoya bayan Trump a tsakiyar birnin ba.
Magoya bayan Trump sun yi ta taruwa a birnin, a
ranakun Asabar na makwanni uku da su ka gabata.
Mutane biyu sun mutu a yayin wata zanga-zanga a yau
Masu zanga zangar sun yi yinkurin tsai da tawagar
motocin, ta wajen tsayawa kan tituna da kuma katse
gadoji.

Portland ya kasance fagen zanga-zanga da dare na
tsawon watanni fiye da uku, tun bayan da ‘yan sanda
su ka kashe George Floyd a Minneapolis. Gabanin
wannan harbin, ‘yan sanda sun yi kame jiya Asabar su
ka kuma shawarci mazauna wajejen su kauce ma
maciyar birnin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *