Kungiyar manyan ma’aikatan jami’o’i ta kasa ta ce dole sai gwamnati ta biya musu bukatunsu za’a bude Makarantu
1 min read
Kungiyar manyan ma’aikatan Jami’o’i ta kasa SSANU ta ce, idan har gwamnatin tarraya ta bude makarantun kasar nan ba tare da cika ma ta alkawuranta ba, shakka babu za ta tsunduma yajin aiki.
Mataimakin shugaban kungiyar Alfred Jimoh ne ya bayyana hakan yayin zantawa da manema Labarai a Jami’ar Badan.
Jami’an tsaro za’a tuhuma kan matsalar batun tsaro-Masari
A cewar sa, idan har gwamnatin za ta duba yiwuwar bude makarantu to kamata ya yi ta kara nazartan biya mata bukatunta, da nufin bai wa dalibai manyan makarantu komawa makaranta.
Makaman da jami’an tsaron Nigeria suke Amfani dasu tsofaffi ne
Alfred Jimoh ya ce, daga cikin bukatun ‘ya’yan kungiyar akwai biyan su alawus-alawus wanda ta ce gwamnatin ba ta biya su ba tun daga shekara ta dubu biyu da tara zuwa yanzu.