July 18, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Masu garkuwa da mutane sun sace mutane 10 a karamar hukumar Doguwa

1 min read

Wasu masu garkuwa da mutane sun kai hari a dajin Falgore, kan hanyar ƙaramar hukumar Doguwa zuwa birnin Kano.

Wani shaidar gani da ido mai suna zakari dauda ya shaidawa Jaridar bustandaily cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 7 na safe, inda masu garkuwar ɗauke da makamai suka tsare kan titi tare da kama mutane.

Ado Musa ya ƙara da cewa lamarin ya rutsa da wasu mutane uku da har zuwa yanzu ba a san inda suke ba, sai kuma wasu da suka jikkata a yayin afkuwar lamarin.

Daga cikin waɗanda suka tsira da raunuka akwai kwamandan Hisbah na ƙaramar hukumar Doguwa Malam saminu Abdukadir wanda lamarin ya rutsa da shi a kan hanyar sa ta zuwa Kano, inda yanzu haka yake ci gaba da samun kulawa a asibiti kamar yadda babban kwamandan Hisbah na jiha sheikh Harun da ya shaidawa bustandaily

Kakakin rundunar ƴan sanda ta jihar Kano DSP. Abdullahi Haruna Kiyawa ya tabbatarwa da Freedom Radio faruwar lamarin, har ma ya ce, tuni rundunar ta Fara bincike akan lamarin

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *