June 23, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mayar da hukumar yiwa ‘yan Kasa Rijista Nimc Ma’aikatar sadarwa

1 min read

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da mayar da hukumar yi wa ‘yan kasa rijista ta NIMC zuwa ma’aikatar sadarwa ta zamani a birnin tarraya Abuja.
Hakan na cikin wata sanarwar mai dauke da sa hannun mai magana da yawun ma’aikatar sadarwa Uwa Sulaiman.
Sanarwar ta bayyana cewa, amincewar mayar da hukumar ta NIMC zuwa ma’aikatar sadarwa ya biyo bayan la’akari da gwamnati ta yi da irin rawar da za ta bayar na samar da dabarun bunkasa harkokin sadarwar zamani.
Sanarwar ta kara da cewa, mayar da hukumar wajen zai taimaka wajen ganin an samu daidaito tsakanin ma’aikatar sadarwa da hukumar NIMC don ba ta damar bibiyar yadda za a samar da hanyoyin sadarwa masu mahimmanci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *