June 23, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Sojojin Najeriya sun ceto mutum 10 da aka yi garkuwa da su

1 min read

Rundunar tsaro ta sojojin Najeriya da ke Abuja ta ce ta samu nasarar
ceto mutum 10 da aka yi garkuwa da su a yankin arewa maso
yammacin ƙasar cikin kwana huɗu.
Rundunar ta bayyana haka ne cikin wata sanarwa da ta wallafa a
shafinta na intanet, inda ta ƙara da cewa dakarunta na rundunar Sahel
Sanity sun kashe tare da kama wasu ‘yan fashin daji.
An ceto mutanen ne a dazuka daban-daban na JIhar Katsina yayin
hare-haren da take kaiwa a yankin daga ranar Litinin, 24 zuwa 28 ga
watan Agusta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *