April 15, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Ambaliyyar Ruwa ta haddasa a sarar amfanin gona na Miliyoyin Nera

2 min read

Gwamnatin Jihar Kebbi da ke arewacin Najeriya ta ce manoman
jihar sun yi asarar shinkafa da sauran amfanin gona, wadanda
kudinsu ya kai fiye da naira biliyan daya sanadiyyar ambaliyar ruwan
da ta faru a sassa daban-daban na jihar.
Hukumomi sun ce ambaliyar ruwan ta mamaye dubban hektocin
filayen noma da gidaje, abin da ya haifar da asarar dukiya a yankunan
da lamarin ya shafa.
Kebbi na daga cikin jihohin da Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta zaɓa
domin bunƙasa noman shinkafa a wani shiri da ta bullo da shi a
shekarun baya. Yanayin da wasu manoma suka fada a jihar ya munana, inda
wasunsu ke ganin cewa ba su taɓa fuskantar matsala kwatan-kwacin
wadda suka samu kansu cikinta ba a cikin wannan damina.
Zaidu Bala Kofa daya ne daga cikin manoman da wannan asara ta
rutsa da su kuma ya ce rabonsu da ganin irin wanann amabaliyar tun
a 2011.
“Rabommu da ganin irin wannan ambaliya tun 2011 saboda wannan
fadama ba mu san yadda za mu kwatanta [girmanta] ba,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa “fadamar ta taso daga ƙaramar hukumar Audi zuwa
Argungu zuwa Birnin Kebbi zuwa Kalgo zuwa Bunza zuwa Ɗakin Gari
zuwa Kokumesi zuwa Bagudu.
“Wannan gaskiya ba ƙaramar asara ba ce.”
Sauran mutanen da suka rasa albarkatun gonarsu a wannan bala’i
sun koka ga gwamnatin jiha da ta tarayya.
Attahiru Maccido, shi ne kwamishinan aikin gona na jihar, ya ce duk
da cewa hasashe ya nuna cewa ambaliyar za ta ci gaba da barna har
zuwa wani lokaci, suna shirin bayar da tallafi a gwamnatance.
“Da ya ke tun kafin yanzu muna da masaniya, ma’aikatar bayar da
agajin gaggawa ta tara dukkanin ma’aikatu domin ganin yadda za a
bai wa mutane agaji,” a cewar kwamishinan.
Noma musamman na shinkafa, na daga cikin manyan abin dogaro ga
al’ummar jihar ta Kebbi tun bayan hawan gwamnati mai-ci ƙarƙashin
shugaban Muhammadu Buhari, wanda ya kudiri aniyar farfado da
bangaren noma bayan rufe kan iyakokin kasar.


Sai dai hadura irin wadannan ka iya mayar da hannun agogo baya
ganin irin dinbin asarar da wannan ambaliya ta haifar ga manoman
yankin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *