April 23, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Gwamnatin Kaduna ta ce bata da hannu game da batan Abubakar Idris

2 min read

Gwamnatin jihar Kaduna a arewa maso yammacin Najeriya ta ce ba
ta da hannu a bacewar matashin nan Abubakar Idris Usman wanda
aka fi sani da dadiyata, shekara ɗaya bayan ɓacewarsa.
Gwamnatin ta bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ta fitar ranar
Litinin. Kwamishinar Shari’a ta Kaduna, Aisha Dikko ta shaida wa
BBC “mu bamu san (wata) maganarsa ba gaskiya, muma yadda kuka
karanta a cikin jarida haka muka karanta.
Ba mu kai shi kotu ba kuma bamu sa a yi wani bincikensa ba, bamu
san komai game da al’amarin nasa ba.” Ta ce a irin wannan yanayin, ana kai wa jami’an tsaro ƙara ne “kuma
ina ji iyalinsa sun kai kara wajen jami’an tsaro su yi musu bincike, a
kan binciken da ‘yan sanda suka yi ne za a ɗauki mataki.” in ji
kwamishinar.
Game da matakin da gwamnatin Kaduna ta ɗauka kan batun ɓatan
Dadiyata kuwa, Aisha Dikko ta ce “‘yan sanda ne suke bincike ba
gwamnati ba, ‘yan sanda sai sun fara bincike kafin gwamnati ta shiga
maganar. ‘Yan sanda suna bincike basu kawo wa ma’aikatarmu ba
kan abin da suka gano.”
Wasu da ba a san ko su waye ba ne suka yi awon gaba da Dadiyata
da tsakar dare daga gidansa da ke birnin Kaduna a watan Agustan
bara, kuma tun sannan ba amo ba labarin Dadiyata.
Kwamishinar ta kuma yi bayani game da wasu da gwamnatin Kaduna
ta shigar da ƙara kansu, “mun kai su ƙara kan maganganun da suka
yi ba gaskiya ba kuma waɗanda ke iya tado rigima a garin.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *