July 16, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Tsadar fulawa na kara haddasa tashin farashin burodi a Najeriya

2 min read

Tsada ko karin kudin fulawa a daidai lokacin da ake kokowa da
sauyin farashin kudin shinkafa na sake haddasa damuwa da
fargabar yadda a kullum farashin abinci ke sake hauhawa a Najeriya.
A ƴan kwanakin nan, kuɗin burodi da duk wasu kayayyakin da ake
hada wa na fulawa na sake kara kudi ba tare da sani dalilin ba.
Karin kudin ba wai ya tsaya kadai ba ne kan fulawa kusan ya shafi
garin tuwo da taliya da alkama.
Wani mazaunin Kano, Ibrahim Sabo ya shaida wa BBC cewa ya yi
mamaki da ya je sayen burodi aka shaida masa cewa farashin ya
sauya.
Ya farashin fulawa yake a yanzu?
Wannan kari ba wai a wuri guda ba ne kusan a duk jihohi da birnin
Tarayyar ƙasar an samu sauyin farashi idan aka kwatanta da
makonin da suka gabata.
Adamu Abdulkadari manajan gidan burodin AMK Kore a Kano ya
shaida cewa BBC cewa a baya suna sayen buhun fulawa kan dubu
10,000 amma yanzu farashin ya kai 13,500. ɗaya?
Adamu ya ce babu wani cikaken bayani da suka samu kan dalilin
karin kudin fulawar, amma kamfanoni na ce musu komai ya kara kudi
ne.
“Ba su ce mana takamaimai ga dalilin tsadar fulawar ba amma
manyan diloli na cewa sinadarann hada kayan fulawa sun kara kudi'”.
Abin takacin ma shi ne bayan ka siya fulawa mai tsada, shi ma
sukari da hoda da yis da sauran kayan hada burodi duk sun yi kuɗi,
in ji Adamu
Manajan ya ce sun tattaunawa a ƙungiyance kan tsadar amma da
alama ba sauyi za a samu ba tunda tsadar ta tilasta dole a yi karin
kuɗin burodin.
”A baya muna bada tallafi ko ragin kudin burodin amma yanzu mun
daina, sannan wayanda basu kara kudi ba sun rage girmar burodin.
Karin bayyani
Burodi kusan abinci kowanne gida ne a Najeriya. Kusan ya fi
kowanne abinci saurin samuwa. Cimakar gidan mai kudi da talaka.
Akwai gidajen burodi da dama a kasar da ke samar da ayyukan yi ga
mutane da dama.
Rahotanni sun nuna cewa Najeriya na cikin kasashe ‘yan gaba gaba
da al’ummar ba su da cimmaka sama da Burodi.
Sai dai ana ta’alaka tsadar da kayan fulawa ke yi da burin da
kamfanonin suka sa kan fulawar da suke fitarwa.
Ana zargin cewa kamfanonin baki ƴan kasashen ketare da ke sarrafa
da sanar da fulawa kusan su suka taka rawa wajen tsadar da kayan
fulawa ke yi a kasar.
Ƴan Najeriya da dama na ganin idan mahukunta suka cigaba da zura
ido kayan abinci na tsada to nan gaba ga mutane da dama abin kai
wa baki zai gaggara.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *