June 13, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

An fara amfani da sabon tsarin biyan kuɗin wutar lantarki a Najeriya

2 min read

Kamfanonin samar da wutar lantarki a Najeriya sun fara amfani da
sabon farashin wutar lantarki daga farkon watan Satumbar 2020.
Matakin ya biyo bayan sauyin da hukumar samar da hasken lantarki
ta Najeriya wato PHCN ta yi.
Sabon tsarin ya karkasa ma su amfani da wutar zuwa gida biyar inda
karfin aljihun kowa ne ma’aunin wutar da za a ba shi.

Ana zaton mutane uku sun mutu bayan da wani gini ya fado a unguwar Rijiyar Lemo a Jihar Kano
Mai magana da yawun kamfanin raba wutar lantarki da ke kula da
jihohin Kano da Katsina da kuma Jigawa, Ibrahim Sani Shawai, ya
shaida wa BBC, cewa an karkasa tsarin ga bangarori daban-daban
ciki har da masana’antu da kamfanoni da ma’aikatun gwamnati da
kuma unguwannin masu hannu da shuni. Sai dai ya ce mutane na da damar komawa matakin koli na samun
wutar lantarki idan suka ga suna da karfin biyan abin da ake caza.

Gobara ta kone tashar Tv ta NTA
”Hakan na nufin cewa daga yanzu iya kudinka iya shagalinka” In ji
Shawai. Rashin wutar lantarki a Najeriya a iya cewa na daga cikin manyan
abubuwan da suka karya lagwan tattalin arzikinta, musamman ma ta
bangaren masana’antu.
Gobara na cigaba da ci kamar wutar daji.
kamfanoni da dama sun rufe harkokinsu a kasar sun koma wasu
kasashen Afirka saboda rashin wutar lantarki a Najeriya kamar yadda
rahotanni suka sha bayyanawa.
Gwamnati ta sha bullo da matakai da dama da zummar magance
matsalar, sai dai har yanzu ‘yan kasar na kokawa a kan wannan
matsala. An warewa bangaren makudan kudade karkashin yarjejeniyoyin da
gwamnati ta cimma da kamfanonin kasashen waje daban-daban da
zummar samar da hasken wutar lantarki, sai dai wasu na ganin cewa
har yanzu bata sauya zani ba.
Gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari, na bugun kirjin cewa ta
samar da karin kuzarin wutar idan aka kwatanta da yadda ta tarar da
ita, amma wasu na cewa ci gaba ne irin na mai hakar rijiya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *