June 13, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Buhari ya kirkiro da Ranar Matasa a Nigeria

1 min read

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da ranar 1 ga watan Nuwamban kowacce shekara a matsayin ranar Matasa.
Ministan wasanni Sunday Dare ne ya bayyana hakan ta shafin san a Twitter yana mai cewa shugaba Buhari ya amice da ranar ne a wajen taron majalisar zartaswa na kasa da aka saba gudanarwa a larabar kowanne mako.
Sunday Dare ya ce shugaba Buhari ya amince da ranar ne da nufin yin gangami da wayar da kan matasa, tare da lalubo hanyoyin ciyar sa su gaba da kuma gyara rayuwar su kasancewar su ne zasu jagoranci kasar nan a nan Gaba.
Taron majalisar zartaswar wanda aka gudanar ta kan Internet dai ya sami halartar mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osibanjo da sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha da sauran Ministoci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *