June 13, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Buhari ya musanta zargin cewa daya daga cikin jami’an gwamnatinsa ya kamu da Corona

1 min read

Fadar shugaban kasa ta musanta labarin da ake yadawa cewa guda daga cikin masu taimakawa shugaba Buhari wato Sarki Abbas ya kamu da cutar Corona.
Hakan na cikin sanarwar da mai baiwa shugaban kasar shawara kan kafofin yada labarai Malam Garba Shehu ya fitar.
Ta cikin sanarwar Garba Shehu ya bukaci ‘yan Najeriya da su yi watsi da wannan jita-jita, yana mai cewa wannan labara ne da bas hi da tushe ballantana makama, yana mai cewa wasu marasa kishin kasane kawai suka kirkiri labarin don haifar da fargaba a zukatan mutane.
Sanarwar ta ce labarin da ake yadawa cewa Sarki Abba wanda makausanci ne ga shugaba Buhari kuma mai taimakwa shugaban kasar kan harkokin cikin gida ya kamu da cutar lamarin da ya sanya ba’a ganin gilmawar sa tsahon makkoni biyu ba gaskiya bane.
Sanarwar dai ta bukaci ‘yan kasar nan da su yi watsi da jita-jitar don kuwa an shirya ta ne da wata manufa mara amfani.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *