July 16, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Gwamnatin Nigeria ta fara shirin samar da wutar da lantarki a karkara

1 min read

Gwamnatin tarayya ta ce shirye-shirye sun yi nisa na samar da wutar lantarki a karkara wanda gidaje a kalla miliyan biyar za su amfana da kudin sa ya kai sama da Tiriliyan biyu karkashin shirin bunkasa harkokin tattalin arziki.
Karamin ministan harkokin wutar lantarki Mr Goddy Jedy-Agba ne ya bayyana hakan yayin kaddamar da wutar Lantaki mai da zata mamaye yankin karu da ke birnin tarayya Abuja.
Mr. Goddy ya ce, gwamnatin tarayya zata baiwa mazauna karkara kulawar da ta dace wajen samar musu da hasken wutar lantarki wanda hakan zai taimaka musu wajen gudanar da kananan sana’o’in dogaro da kai.
Mr Goddy ya kara da cewa, mazauna karkara sun fi mayar da hankali wajen biyan kudin wuta fiye da mazauna cikin gari, a don haka a yanzu za su samu wadatacciyar wutar lantarki don magance matsalolin su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *