June 13, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Rushewar gida ta jikkata mutane uku tare da rasa ran yaro ɗaya a jihar Kano

1 min read

Lamarin ya faru ne da asubahin yau Talata sakamakon ruwan sama
da iska da aka tafka, inda gidan wani Magidanci mai suna Alhaji
Umar Baba ya ruso a kan ƴaƴansa, kuma a lokacin da magidancin ya
je don ganin abin da ya faru sai ginin ya ƙara ruftawa da shi.

Mai ɗakin magidancin Aisha Umar ta shaidawa bustandaily cewa
mai gidan ta da ƴaƴanta biyu suna asibiti ana ci gaba da duba
lafiyarsu, bayan da maƙota suka kawo musu ɗauki.

Sai dai, ɗanta guda ɗaya Muhammad Umar ɗan shekara 12 ya rasa
ransa.
Wani daga cikin maƙota da suka kai musu ɗauki mai suna
Muhammad Ibrahim ya shaida cewa, ya fito zuwa
masallaci kawai sai ya ji ƙarar faɗuwar ginin wanda hakan ya sanya
ya gayyato al’umma suka kawo musu ɗauki.
Hukumar kashe gobara ta Kano ta tabbatar da faruwar al’amarin
kamar yadda kakakinta Sa’idu Muhammad Sule ya tabbatar wa jaridar bus tan daily yana mai cewa akwai gurare da ya kamata al’umma su lura dasu sosai musamman a damunar bana.
Sa’idu Sule ya kuma nemi al’umma da su riƙa ɗaukar mataki a duk
lokacin da suka lura da gini ya fara nuna alamun zaftarewa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *