September 22, 2023

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Sojojin Kamaru sun kashe wasu ‘yan awaren yankin renon Ingila

2 min read

Jami’an tsaro a Kamaru sun ce sun kashe wasu masu tada-kayar-
baya 17 tare da cafke mutum 7 da ke dauke da wasu kayan fashewa
a yankin renon Ingila.
Jami’an sun kai farmakin ne karkashi atisayen ”Operation Boyo 1″
wanda ya ba su damar kwashe kwanaki 6 a cikin daji suna bin takun
‘yan aware da ke kai farmaki a kan jama’a.
Kusan sojoji 450 ne ma’aikatar tsaro ta tura daji inda suka rinka
hawa tsaunuka da tafiya cikin ruwa kana kuma suka rinka nitsewa a
cikin tabo da zummar mayar da tsaro da zaman lafiya a yankin renon
Ingila.
A wannan karon ne dai jami’an tsaron suka samu nasarar dawowa da
dumbin ganima kamar makamai da wasu tarin kayayyaki da ma
masu masu fafutukar mutum bakwai.
Kwamandan shiyya ta 51 na rundunar sojin kasar, ya ce wannan
kadan ne daga cikin daga cikin irin kayayyakin da jami’ansu suka
tattaro a yayin farmakin da suka kai.
Ya ce a yayin farmakin sun yi karo da sansanoni na masu fafutkar da
dama.

Sojoji sun yi juyin mulki bayan kifar da gwamnatin Ibrahim Boubacar Keïta a kasar Mali
Sakamakon wannan nasara da sojojin suka samu a kan masu
fafutukar, hukumomi suka yi kira ga jama’a da su rinka ba su hadin
kai domin kai wa ga irin wadannan mutane masu fafutuka a duk inda
suke.

Sojojin Najeriya sun tarwatsa ‘yan fashi a Kaduna.
A yanzu haka dai, mahukuntan sun umarci iyaye da su mayar da
‘ya’yansu makarantu daga ranar 5 ga watan Oktoba da ke tafe.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *