July 16, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Ambaliyar ruwa ta kashe mutum 15 a Sokoto

1 min read

An tabbatar da mutuwar mutum 15 sakamakon wata ambaliyar ruwa da
ta faru a wasu ƙananan hukumomi shida a jihar Sokoto.
Jaridar Daily Trust a Najeriya ta ruwaito hukumar bayar da agajin
gaggawa ta ƙasar wato NEMA inda ta ce sama da mutum 27,000
wannan bala’i ya shafa.
Ƙananan hukumomin da bala’in ya shafa sun haɗa da Goronyo da
Rabah da Arewacin Sokoto da Wamakko da Silame da Binji.
Rahoton da jaridar ta samu daga hukumar ya nuna cewa mutum 5,254
sun rasa muhallansu inda wasu mutum 12 kuma suka samu raunuka
sakamakon rugujewar gine-gine.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *