June 13, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

An yi kashe-kashe tsakanin sojojin Najeriya da mayaƙan ISWAP a jihar Borno

2 min read

Rahotanni daga arewa maso gabashin Najeriya na cewa an samu
ƙarin tashe-tashen hankali tsakanin sojojin Najeriya da mayaƙan
ƙungiyar ISWAP wadda ta balle daga ƙungiyar Boko Haram.
Ƙungiyar masu tayar da ƙayar baya ta ISWAP ta ce mayaƙanta sun
kashe sojojin Najeriya aƙalla 20 a hare-hare biyu da suka kai kan
sojojin a jihar Borno da ke arewa maso gabashin ƙasar.
Rahotanni na cewa masu tayar da ƙayar bayan cikin motoci da aka
girke manyan bindigogi a kansu, sun kai hari ne a wani sansanin soji
da ke Magumeri, kimanin kilomita hamsin daga Maiduguri babban
birnin Jihar ta Borno.
Me ISWAP ta ce?
Cikin wata sanarwa, kungiyar ISWAP wadda ta ɓalle daga Boko
Haram, ta yi ikirarin cewa mayakanta sun kashe sojoji goma da kuma
kwace makamai da motocin soji a yayin arangama da suka yi.
Kungiyar ta kuma yi ikirarin cewa ta kashe wasu karin sojoji 10 a
wani kwanton-bauna kan ayarin sojojin a kusa da kauyen Kuros-
Kauwa da ke yankin Baga.
Duka lamuran biyu sun faru ne a ranar Talata. Kawo yanzu babu
wata majiya mai zaman kanta da ta tabbatar da ikirarin masu tayar da
kayar bayan.
Sai dai kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito cewa
majiyoyinsa sun tabbatar masa da cewa sojoji tara mayakan suka
kashe a Magumeri.
Me rundunar sojin Najeriya ta ce?
Rundunar sojin Najeriya ba ta ce uffan ba kan lamarin, kuma duk
kokarin da BBC ta yi na jin ta bakinta ya ci tura domin kakakin
hedikwatar tsaron Najeriya, Manjo-Janar John Enenche, bai amsa
kiraye-kiraye ta wayar tarho ba.
To sai dai a wata sanarwa, rundunar sojin ta yi ikirarin kashe
mayakan kungiyar ta ISWAP a wani farmaki ta sama da dakarunta
suka kai da jiragen yaki kan matsugunan masu tayar da kayar bayan
a kauyen Kaza, kusa da Gulumba-Gana a yankin Bama cikin jihar ta
Borno.
Shi ma farmakin, a ranar Talata sojojin suka kai, wato ranar da
kungiyar ta ISWAP ta yi ikirarin kashe sojojin.
A watan Agustan da ya gabata ma sai da Ƙungiyar IS ta ce ta kashe
sojojin Najeriya guda bakwai a garin Kukawa da ke jihar Borno a
arewacin Najeriya, yayin da rahotanni suka ce kuma mayakan sun
kuma yi garkuwa da mutane da dama a garin.
A baya-bayan nan dai sojojin Najeriya na kara ƙaimi a hare-hare ta
sama da suke kai wa kan masu tayar da kayar baya a yankin Tafkin
Chadi.
Ayyukan tayar da kayar baya na kungiyar Boko Haram da kuma
ISWAP da ta ɓalle daga cikinta, sun yi sanadiyyar mutuwar mutum
fiye da 30,000 da kuma raba miliyoyi da muhallansu a ƙasashen
Najeriya, da Nijar da Kamaru da kuma Chadi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *