June 13, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Auwal Mudi ya nayin babakere da kudaden kungiya tare dakin gudanar da zaben kungiyar yakasai Zumunta

2 min read

Wasu Matasan Unguwar Yakasai dake nan Kano, sun zargi daya daga cikin Shugabanin kungiyar su, ta Yakasai Zumunta da yin babakere, da wasu kayayyakin kungiyar tare da kin amincewa a gudanar da zaban shugabanin kungiyar.

Malamai na taimawa cin hanci da rashawa a Nigeria
Matasan sun ce,sakataren kungiyar,Kwamarad Auwal Mudi Yakasai yaki amincewa a gudanar zabe a kungiyar,wanda a baya an nada shi a matsayin Sakataren Riko domin ya gudanar zaben shugabanin kungiyar,amma yaki aiwatar da hakan.

Malamai na taimawa cin hanci da rashawa a Nigeria
Matasan sun ce Sakataren Kungiyar ambashi wa’adin wata shida da ya gudanar da zaben Sababbin shugabanin kungiyar,amma yau tsahon Shekara goma kenan yaki amincewa a gudanar da zaben kamar yada matasan suka bayyana da bakinsu.
Game da koken Mutanan ne ya sanya muka tuntube Sakataren Kungiyar Kwamared Auwal Mudi,Yakasai domin tabakin sa kan wannan batu.

Malamai na taimawa cin hanci da rashawa a Nigeria
Kwamared Auwal Mudi ya ce bashi damar gudanar da zabe a kungiyar kasancewar iyayen kungiyar ne,kawai suke da damar gudanar da zaben kungiyar.

Alhaji Sani Kwangila Yakasai daya ne daga cikin iyaye a kungiyar ta Yakasai Zumunta,yayi Karin gaske game da wannan dambarwa a kungiyar.
Ka zalika ya bukaci matasan dasu tallafawa kungiyar ba hayaniya domin samun cigaban unguwar Yakasai baki daya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *