Gwamnatin Tarayya ta bada umarnin bude Makarantu baki daya
1 min read
Babban jami’i a kwamitin Shugaban kasa mai yaki da cutar corona Dakta Sani Aliyu ne ya bayyana haka a Abuja.
Ya ce Makarantun kasar nan baki daya an amince dasu bude makarantunsu domin cigaba da karatu yadda aka saba.
Sani Aliyu ya ce daga furamari har sakandire zasu cigaba da gudanar da karatu.