June 12, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Kashi 30 na ‘yan Najeriya ba su da lafiyar ƙwaƙwalwa – Kwararru

3 min read

Kwararru a fannin lafiyar kwakwalwa a Najeriya na cewa jama’a da
dama na da matsalolin kwakwalwar da ba su san suna da su ba
wadanda ka iya kai wa ga hauka.
Mutane da dama na fama da larura a kwakwalwarsu amma ba tare
da sun sani ba ko kuma sun san da matsalar amma sai su nuna ba
ta faruwa.
Dr Auwal Abubakar Fatihu na fannin kula da masu tabin kwakwalwa
a asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano da ke birnin Kano a
Najeriya ya ce “ina mamakin yadda za ka jama’a na tururuwa zuwa
ganin likita sakamakon samun larura a hantarsu ko koda ko ciki da
ido da dai sauransu amma idan aka yi batun lafiyar kwakwalwa sai
mutane su yi zaton komai kalau ba tare da sun je wurin likita ba.”
Hakan ne ya sa “wata kididdiga ta nuna cewa kashi 30 na masu zuwa
asibiti a kowane gari a Najeriya na fama da matsalar kwakwalwa da
ake kira psycological problems”, in ji Dr Auwal.
A Najeriya da kasashen Afirka danganta mutum da samun rashin
lafiyar kwakwalwa tamkar bayyana mutum da mahaukaci ne inda a
wasu lokuta irin wadannan furucin kan kai ga yin shari’a.
To sai dai likitocin kwakwalwa sun ce ba haka lamarin yake ba
kasancewar idan za a yi zube-ban-kwaryata to da dama daga cikin
mutane ba su da lafiyar kwakwalwa.
Alamomin larurar kwakwalwa
Kwararren kan fannin lafiyar kwakwalwa, Dr Auwalu Fatihu Abubakar
ya zayyana wasu alamomi karkashin abin da ya kira sauye-sauye
wajen yadda mutum yake gudanar da al’amuransa, a matsayin
alamomin larurar kwakwalwa.
Rashin son shiga mutane
Rashin bacci
Rashin magana
Rashin tsaftar jiki
Yawan fada
Rashin hakuri
Alamar damuwa
Tunanin jama’a sun tsane shi.
Abubuwan da ke haddasa larurar kwakwalwa
Shiga yanayin kunci sakamakon zamantakewa a gida ko wurin
aiki ko kuma kasuwa
Kunci ko matsi a rayuwa da ake kira ”Stress”
Sannan akwai yanayin mutum da ake kira ‘personality’ inda mai
wannan halayya yake da saurin damuwa sakamakon wani abu.
Alakar larurar kwakwalwa da hauka
Dr Auwal ya ce alakar da ke tsakanin larurar kwakwalwa da ciwon
hauka shi ne ciwon hauka cuta ce daya daga cikin larurorin
kwakwalwa.
Sai dai masanin lafiyar kwakwalwar ya ce larurar kwakwalwa ka iya
jefa mutum cikin yanayin hauka daga bisani.
“A kan samu yanayin da mutum musamman matasa a wannan
zamanin kan samu kansu a yanayin damuwa da matsi da kuncin
rayuwa, abin da ke sanya su su fada yanayin shaye-shaye domin
samun mafita. Hakan daga bisani na sa su samu ciwon hauka.”
Dangane da abubuwan da suke sanya hauka, Dr Auwalu ya ce “akwai
dalilai masu yawa da ke sanya mutum ya zama mahaukaci amma
kuma ana gado daga dangi da ake kira ‘familial factor’ sannan kuma
ana samun hauka ta hanyar kaddara.
Ana kuma samun hauka sakamakon matsi na rayuwa da shaye-
shaye da kuma sakamakon buguwa yayin wani hatsari.”
Mafita
Hanyoyin magance matsalolin kwakwalwa musamman wadanda ba
ciwon hauka ba ne su ne guda biyu:
Sauya tsarin rayuwa wato idan mutum yana da daukar al’amura
da zafi to ya yi wa kansa fada domin ganin yadda zai sassauta
Tuntubar likitoci domin samun shawarwari kan yadda za a shawo
kan matsalar kafin ta ta’zzarax.
Wani al’amari da ake ganin ya taba lafiyar kwakwalwar mutane a
baya-bayan nan shi ne annobar cutar korona wadda ta jefa al’ummar
duniya a halin dimuwa da rashin tabbas.
A kasashen Turai da wadanda suka ci gaba, jama’a sun yi ta
tururuwa zuwa wurin likitocin kwakwalwa domin duba lafiyar
kwakwalwar tasu baya ga rubuce-rubuce da masana suka yi ta yi kan
yadda al’umma kan yadda za su kare kansu daga fadawa yanayin
samun tabin kwakwalwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *