July 12, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Kungiyar Daliban Nigeria ta bukaci Buhari da ya sauka daga makaminsa

1 min read

Kungiyar daliban Ngeria wato National Association of Nigerian Students

Ta yi fatali da matakin gwamnatin Nigeria na karin farashin manfetir.

Shugaban kungiyar Kowe Odunayo Amos, ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar a Abuja.

Ya kuma ce wajibine shugaban kasa Buhari ya sauka daga mukaminsa a sakamakon gazawa ta bangarori da dama da suka hadar da tashin kayan masarufi da karin kudin manfetir dana wutar lantarki dana kashe-kashen mutane da sauransu.

Gwamnatin Nigeria ta sanar da karin farashin manfetir
Haka zalika sanarwar ta bukaci manyan jagororin gwamnatin Buhari da suma su sauka daga mukamansu cikin hanzari.

Kungiyar dillalan manfetir ta kasa reshen kano Ipman ta ce zata sanar da sabon farashin man a yau
A jiya ne dai gwamnatin Nigeria ta sanar da karin farashin manfetir din daga 148 zuwa Naira 151.51.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *