June 18, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Kungiyar dillalan manfetir ta kasa reshen kano Ipman ta ce zata sanar da sabon farashin man a yau

1 min read

ƙungiyar dillalan man fetur shiyyar jihar bata sanar da farashin da ta tsayar wajen sayar da man ba.
Shugaban ƙungiyar dillalan man ta ƙasa shiyyar Kano Alhaji Bashir Ɗan Malam ya shaida wa jaridar bustandaily cewa, kamfanin NNPC ya riga ya bada sanarwar yin ƙari, a don haka ba su da zaɓi sai dai suma su yi ƙarin farashin.

Bashir Ɗan Malam ya ce, suna yin nazarin yadda za su ci riba a sana’ar su, kuma tuni suka fara tattaunawa zuwa kowane lokaci daga yanzu za su bada sanarwar farashin da zasu riƙa sayar da man a nan Kano.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *